Connect with us

LABARAI

Gasar AFCON: Attajiran Nijeriya Sun Yi Wa Tawagar “Super Eagles” Alkawarin Kyauta

Published

on

Manyan Attajiran Nijeriya guda biyu, Aliko Dangote da Femi Otedola sun yiwa Yan wasan tawagar “Super Eagles” na Nijeriya dake gasar cin kofin Afirka a Masar alkawarin kudade idan sun samu nasara a sauran wasannin su guda biyu da suka rage, bayan nasarar da suka samu a wasan daf da na kusa da na karshe kan Afirka ta kudu.

Yayin ziyarar da suka kaiwa kungiyar a otel din da suke a Birnin Alkahira, Aliko Dangote yayi alkawarin biyan Dala 50,000 kan kowanne kwallo guda da kungiyar ta jefa a wasannin da za suyi nan gaba, yayin da Femi Otedola yayi alkawarin Dala 25,000 kan kowanne kwallo guda.

Kafin wannan alkawarin, wani attajirin Nijeriya mai harkar mai, Captain Hosea Wells Okunbo ya yiwa kowanne dan wasa guda alkawarin Dala 20,000 idan sun doke kamaru kuma ya biya su bayan nasara da suka samu, kana shima Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu ya baiwa kowanne Dan wasa Dala 5,000 saboda gagarumar nasara da suka samu akan Kamaru.

Haka ma kamfanin man AITEO dake hadin gwiwa da Hukumar kwallon kafar Nijeriya ta biya Dala 25,000 akan kowanne kwallo guda da Nijeriya ta jefa a wasan Kamaru.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!