Connect with us

LABARAI

Gwamna Zulum Zai Fallasa Masu Hannu A Bashin Biliyan Biyu Na CBN A Borno

Published

on

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce a cikin ’yan kwanakin nan gwamnatin jihar za ta bankado ta’asar naira biliyan biyu (N2bn) da wasu mazambata suka handame a jihar, tare da gano masu hannu cikin wannan badakalar kudin rance wadda babban bankin Nijeriya (CBN) a karkashin shirin bayar da lamuni ga yan jihar.

Gwamnan ya bayyana daukar wannan matakin ne da yammacin ranar Laraba, a sa’ilin da yake karbar bakuncin tawagar babban bankin CBN da ke birnin Maiduguri, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa.

Tawagar bankin CBN ta yi wa Gwamnan karin haske dangance da wuraren da ya dace gwamnatin sa ta fi mayar da karfi wajen zaburar da tattalin arzikin jihar a cikin gaggawa, tare da nuna rashin jin dadin yadda al’ummar jihar suka kasa biyan bashin da bankin ya basu na naira biliyan biyu (N2bn), a karkashin shirin bai wa kanana da matsakaitan sana’o’i a lamuni a shekarar 2015.

Kamar yadda babban jami’in babban bankin kasa dake birnin Maiduguri (Controller), Lawal Tijjani ya bayyana, babu ko da mutum daya daga cikin wadanda suka karbi bashin da ya nuna alamar biyan wadannan kudade, duk da dogon lokacin da aka dauka da bayar da shi.

Da ya ke mayar da martani dangane da kememen da wadanda suka karbi bashin suka yi, Gwamnan jihar Borno Farfesa Umara Zulum ya bayyana lamarin da cewa gwamnatin sa ba za lamunta da wannan ba, kuma zai sa kafar wando guda da duk wanda yake da hannu a badakalar.

Bugu da kari kuma Gwamnan ya ce yana da masaniya dangance da irin wannan abin kunya da wasu jami’ai da manyan mutane a jihar ke aikata wa, tare da bayyana cewa gwamantin sa ta dauki matakan gudanar bincike tare da damke dukkanin masu hannu a cikin wannan zamba cikin aminci a harkar kudade.

“Kun fadi gaskiya dangane da jama’ar jihar Borno, kan cewa basu da anniyar biyan wannan bashin da aka ba su,” Ya nanata.

“A cikin yan kwanakin nan,  gwamnati za ta bude shafin bankado sunayen baki dayan wadanda suka ci gajiyar wannan bashi na Naira biliyan biyu, za mu matsa su har sai sun amayar da kudaden kuma mu marar da kudin ga masu su.

“Sannan kuma ba abu ba ne mai yuwuwa, mutum ya dauka kan cewa haka lamurra zasu gudana irin yadda yake so, a matsayin mu na mutane. Haka kuma sanin kowa ne bisa ga halin da matsalar tsaro ta jefa mu a ciki, wanda ban san ta wane dalili ne wani mutum zai yi kememe ya ce ba zai biya bashin kudi kuma ya ki mayarwa, saboda haka zamu kalli wannan lamarin tare da tsara yadda za a biya bashin.

“Duk da na san mutane da yawa da ke da hannu dumu-dumu a kan wannan kudin, amma su ka yi gum da bakinsu. Kuma zamu kamo wadannan mutanen don su bayar da bahasi, sannan akwai wasu daga ciki wadanda su ka shiga wata rigar kariya wajen tabka wannan zambar, wanda ai tuni mun wuce nan, kuma za mu yaye kariyar da su ke takama da ita,” in ji Gwamna.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: