Connect with us

KIWON LAFIYA

Kananan Asibitoci Na Iya Maganin Kashi 70 Na Matsalolin Lafiya – Sarkin Shonga

Published

on

Sarkin Shonga a jihar Kwara Haliru Yahaya ya bayyana cewar kashi 70 na matsalolin da suke shafar kula da lafiyar al’umma, a jihar, kananan asibitoci za su iya daukar wannan nauyin.

Sartkin ya yi bayani ne a wajen taron zango na farko na taron daya shafi mata da kuma Jarirai, da kuma makon yara a asibitin Tanke da yake a karamar Hukumar Ilori ta Kudu ranar Laraba ta makon daya gabata.

Ya bayyana cewar ba su kananan asibitocin kudaden da zasu tafiyar da kansu, da kuma biyan albashin ma’aikata, sune matsalolin da gwamnatin jihar take fuskanta.

Ya kara bayanin shi irin halin da “ Su asibitocin suke abin

takaici ne ga kuma yadda wasu cututtuka suke barkewa lokaci zuwa lokaci.”

Mista Yahaya ya bayyana cewar saboda a taimaka ma kokarin da gwamnatin jihar take yi, tako wanne mataki ne aka kafa shi yasa su masu sarautun gargajiya na jihar, suka ga cewar da akwai bukatar da a rika wayar da kan al’umma, dangane da bayar da hadin kai na allurar rigakafi.

Kamar dai yadda Sarkin ya bayyana yana iya tunawa jihar, a shekarunn baya, Kwara ta kan kasance wadda yakamata ayi koyi da ita, yadda take tafiyar da asibitoci da kuma yadda suke yin aikin nasu, amma kuma rashin yadda ba a basu isassun kudade ga kuma rashin biyan albashin ma’aikata su ne su ka kasance matsalolin da suke kawo cikas na kula da lafiyar al’umma matakin farko.”

Ya kuma kara jaddada aniyar su Sarakunan gargajiya na jihar, su cigaba da wayar da kan al’ummarsu akan yadda za su kula da lafiyar jikinsu.

Sarkiun kuma ya yui kira da gwamnan jihar Abdulrahmman Abdulrazak, da cewar ya farfado da bangarorin kula da lafiyar al’umma matakin farko na jihar.

Kamar dai yadda Basaraken ya bayyana cewar idan aka samu jure ma shi al’amarin na wayar da kan al’umma, yin hakan  zai taimaka matuka, wajen rage wasu cututtuka da su daman a iya maganin su, da kuma barkewar annobar cututtuka, sai kuma al’amarin da ya shafi mutuwar mata da kananan yara.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: