Connect with us

JAKAR MAGORI

Kisan Mutum 17: ’Yan Sanda Sun Cafke ’Yan Sa-kai Hudu A Katsina

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Katsina ta samu nasarar cafke ‘yan kungiyar sa-kai guda hudu, a kauyen Kwatawa cikin karamar hukumar Safana ta jihar, bisa mutuwar fararan hula guda 17. Wadanda a ke zargin dai su ne, Abdullahi Abubakar dan shekara 30, Lawal Abubakar dan shekara 28, Abdusalam Sani dan shekara 35 da kuma Salisu Isah mai shekaru 38.

Majiyarmu ta labarta mana cewa, a ranar Talata ce, wadanda da a ke zargi su ka mamaye wani rugar Fulani, sakamakon kashe musa mambobinsu guda uku  da ‘yan bindiga su ka yi. Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, a ranar 7 ga watan Yuni ne, a ka samu barin bindigogin kirar AK47, a yankin Illelai da ke cikin wannan karamar hukuma, inda a ka kashe ‘yan kungiyuar sa-kai guda uku. ‘Yan kungiyar sa-kai da a ka kashe dai su ne, Ashiru Mansir, Muddaha Mandir da kuma Jabiru Mansir. An bayyana cewa, wadanda a ke zargin sun kai ramuwar gayya ne a kan kashe musu ‘yan uwa da a ka yi. Sakamakon wannan farmaki da su ka kai, mutum 17 su ka rasa rayukansu.

Sakamakon bincike da ‘yan sanda su ka gudanar, ya ga cafke ‘yan kungiyar sa-kai guda hudu,. wadanda a ke zargin su na da hannu a kai wannan farmakin. Tuni a ka gurfanar da wadanda a ke zargin a gaban kotu, inda a ke tuhumar su da laifin hada kai domin aikata laifi da kuma laifin kisan kai wanda ya saba wa sashe na 97 da 221 na dokar fanal kot. An dai gurfanar da su a gaban babbar alkalin kotun Jihar Katsina, Mai shari’a Hajiya Fadile Dikko. Ta bayar da umurnin a cigaba da tsare wadanda a ke tuhuma har sai ranar 22 ga watan Agusta na shekarar 2019. Wannan umurni dai ya biyo bayan bukatar da lauyan ‘yar sanda mai gabatar da kara, Sajan Lewal Bello, ya yi, inda ya bayyana cewa, ‘yan sanda su na bukatar lokaci domin su kammala bincike a kan lamarin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: