Connect with us

JAKAR MAGORI

Kotu Ta Daure Wani Bakanike Wata Shida Bisa Laifin Satar Naira 3,000

Published

on

A ranar Laraba ce, wata babbar kotu da ke garin Jos wacce ta ke da zama a yankin Kasuwan Nama, ta daure wani makanike mai suna Abdullahi Zakari dan shekara 19 da haihuwa, na tsawan wata shida a gidan yari, bisa laifin satar kudi naira 3,000. Alkali mai shari’a Mista Lawal Suleiman, shi ya yanke masa hukunci, bayan ya samu wanda a ke tuhuma da laifin da a ke tuhumar sa da shi na sata. Suleiman ya bai wa wanda a ke tuhuma zaben biyan tarar kudi na naira 6,000.

Tun da farko dai, lauya mai gabatar da kara, Ibrahim Gokwat, ya bayyana wa kotu cewa, an kai rahoton faruwar lamarin ne a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Laranto ranar 27 ga watan Yuni, ta hunnun Aminu Shehu, wanda ya ke zaune a yankin NEPA kan titin Zariya cikin garin Jos. Gokwak ya kara da cewa, a ranar 6 ga watan Yuni, wanda ya kai korafin ya fita daga gidansa domin a amso wasu kudi daga wurin wakilinsa, ya na kan hanyar dawowa kenan sai wanda a ke tuhuma ya hada baki da wasu mutum uku. Ya bayyana wa kotu cewa, wanda a ke zargin ya mari wanda ya kawo korafin a fuskansa har sai da ya samu rauni. Ya kara da cewa, a wannan lokacin dai sun amshe masa kudi naira 3,000. Lauyen ya bayyana wa kotu cewa, lokacin da ‘yan sanda su ka gudanar da bincike, sai wanda a ke tuhuma a amsa laifin da a ke zargin sa da shi. Lauyan ya cigaba da cewa, wannan laifi ne wanda ya ke da hukunci a sashe na 239 da kuma 272 na dokar laifuka ta Jihar Filato.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: