Connect with us

RIGAR 'YANCI

Kumo Ya Zama Kakakin Majalisar Matasa Ta ‘Youth

Published

on

A makon jiya ne aka zabi Khalid Ahmed Kumo a matsayin Kakakin majalisar Matasa reshen jihar Gombe ta ‘Youth Parliament’. Kumu dai shi Mamba ne da ke wakiltar mazabar Akko ta tsakiya a jihar Gombe a karkashin majalisar.

Zabin Kumo a matsayin Kakakin majalisar reshen jigar Gombe, na zuwa ne biyo bayan shigar da kudurin zabinsa da mambar da ke wakiltar Kaltungo ta Gabas, Afiniki Nuhu Gabriel ra yi a harabar kwaryar majalisar da ke Gombe, wanda ya samu mara baya daga dan majalisar da ke wakiltar Yamaltu Deba ta Yamma, Hon. Sulaiman Idris Puma.

Kuma ya samu kuri’u 9, inda ya kayar da abokin takararsa na kusa Aliyu Abdulhamid Yakubu wanda ya samu kuri’u 7, a yayin da kuma na uku daga cikin ‘yan takarar kujerar Aliyu Abduljalal Hassan ya samu kuri’u babu ko guda.

Gabanin ya zama Kakakin majalisar, Kumo dai shine Daraktan sashin kula da ilimi da hada kan dalibai na majalisar ci gaban matasan Afirka, African Youth for Debelopment Commission (AYDEC).

Wakilinmu ya shaido mana cewar a ofishin mataimakin Kakakin majalisar ta matasa kuwa, Afiniki Nuhu Gabariel da ke wakiltar Kaltingo ta yamma ce ta lashe kujerar da kuri’u 10, inda ta nana abokin takararta mai samun kuri’u 7 wato Usman Adamu Bojude, shi kuma Fahad Bundi bai samu kuri’u ko daya ba.

Jim kadan bayan kammala zaben, magatakardar majalisar wanda ya samu wakilcin Daraktan kula da harkokin majalisar Mista Yusuf Burto ya rantsar da su a cikin kwaryar majalisar dokokin matasa ta jihar Gombe.

A jawabinsa na amsar kujerar, Kakakin majalisar Khalid Kumo ya gode wa majalisar matasan a bisa wannan damar da suka bashi, yana mai shan alwashin kyautata shugabanci domin ci gaban matasa a jihar Gombe.

“Ina son na yi amfani da wannan damar wajen nuna gayar godiyata ga abokaina, Honorabul mambas na majalisar matasa a bisa kwarin guiwar da suke da shi a kaina da bani wannan damar, Allah ya bani ikon kyautata musu da sauke nauyin da ke kaina,” A cewar shi.

Kumo ya gode wa ma’aikatar matasa a bisa goyon bayan da suke baiwa majalisar matasan, “Ina kuma kara jaddada godiyarmu ga ma’aikatar matasa na jihar Gombe bisa cikakken goyon bayan da suke baiwa majalisar matasa na jihar Gombe,” in ji Kumo.

Sabon Kakakin majalisar matasan ya nemi abokan takararshi da su hada hannu waje guda domin tabbatar da kai majalisar zuwa mataki na gaba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: