Connect with us

RAHOTANNI

Lauya Ya Nemi Da A Rika Yi Wa Masu Fyade Daurin Rai Da Rai

Published

on

Wani shahararren Lauya mazaunin Ilorin ta Jihar Kwara, Abdul Gegele, ya yi kira ga gwamnatoci a dukkanin matakai da su kafa dokar zartarwa da masu laifukan aikata fyade da hukuncin daurin rai da rai domin a rage yawan aikata wannan mummunan aikin a cikin al’umma. Gegele ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba, lokacin da yake Magana da kamfanin dillancin labarai na kasa a Ilorin.

A cewar shi, Nijeriya tana baya can a kan hukunta masu aikata fyade, duk da yanda abin ke kara kazanta a cikin kasar.

Ya bukaci gwamnatoci a dukkanin matakai da su tabbatar da an yi gyara a kan dokar hukunta masu aikata fyade, domin ta karfafa hukunci a kan masu aikatawan.

“Tilas ne a sanya hukunci mai tsanani a kan masu aikata fyade, saboda masu aikatawan suna kara yawaita ne a Nijeriya. Lokaci ya yi da za mu ce a’a, ga masu aikata fyade, fyade laifi ne mai tsannani da ya zama tilas a kawar da shi daga cikin al’umma. Bai kamata a rika kwarzanta masu aikata fyade ba, ya kamata a rika yi masu hukunci ne mai tsanani domin tabbatar da zaman lafiyar al’umma.

Lauyan ya kuma bukaci wadanda masifar fyaden ta auka masu da su rika fitowa sarari suna yin Magana, su daina kyamatar kansu, domin a samu damar hukunta masu laifin yanda ya kamata. Su kuma daina tunanin su kashe kansu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: