Connect with us

WASANNI

Liverpool Za Ta Taya Asensio Fam Miliyan 67

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta shirya tsaf domin taya dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Marco Asensio, fam miliyan 67 a kokarin da kociyan kungiyar yakeyi na ganin ya sake lashe kofin zakarun turai na shekara mai zuwa.

Har kungiyar Liverpool, wadda ta lashe kofin zakarun turai na shekarar data gabata bata sayi dan wasa ba a wannan kasuwar duk da cewa ‘yan wasanninta guda biyu, Alberto Moreno ya koma Billareal sai kuma Daniel Sturidge wanda har yanzu bai samu kungiya ba amma kuma Liverpool din ta sallameshi.

Sai dai kociyan na Liverpool, Jurgen Klopp, yana fatan zai sayi sabon dan wasa kuma dan wasan tsakiya ake ganin yake bukata domin taimakawa ‘yan wasansa na gaba wato Sadio Mane da kuma Muhammad Salah.

Tuni aka bayyana cewa Klopp ya bayyana dan wasan Real Madrid, Marco Asensio, a matsayin dan wasan da zai nema wanda yake ganin shine zai taimakawa kungiyar tasa musamman a kokarin da yakeyi na lashe gasar firimiya a kakar wasa mai zuwa.

Asensio dai bai buga wasanni da yawa ba a kakar wasan data gabata a Real Madrid sakamakon canje canjen da aka samu na masu koyarwa sai dai hakan baisa farashin dan wasan dan asalin kasar Sipaniya ya canja ba.

Real Madrid dai tana fatan sayar da wasu daga cikin ‘yan wasanta domin samun kudin da zata tunkari Manchester United a kokarin da takeyi na ganin ta dauki dan wasa Paul Pogba wanda ya nuna cewa yanason komawa Real Madrid.




Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: