Connect with us

LABARAI

Magudin Jarabawa: An Kone Wayoyin Miliyoyin Kudi Na Daliban Kwalejin Ibadan

Published

on

Hukumar gudanarwar Kwalejin Kimiya Da Fasaha ta Ibadan da ke jihar Oyo ta kone wayoyin salula na kimanin Naira miliyan 15 da su ka kwace daga hannun wasu daliban makarantar da ake zargin da yin amfani da su a lokutan jarabawa.
Mataimakin Shugaban Kwalejin, Bayo Oyeleke wanda ya jagoranci aikin kone wayoyin salular a jiya Laraba, ya sanar da manema labarai cewa a cikin shekara guda da ta gabata hukumar makarantar ta kwace wayoyin daliban da ake zargi da satar jarabawa.
Ya kara da cewa, a dokar jarabawar makarantar ba a yarda dalibi ya shiga dakin jarabawa da wayar hannu ba don haka hukumar makarantar ta dauki matakin kone wayoyin domin kawar da matsalar magudin jarabawa a tsakanin dalibai a makarantar
Oyeleke ya ce, ‘Manufarmu a nan ita ce mu tabbatar da mun yaye dalibai masu nagarta da kuma tarbiya, wadanda suka yi aiki tukuru domin samun kwalin makarantarmu, ba macuta ba’.
‘Akwai dokokin da makaranta ta kafa dangane da rubuta jarabawa, duk dalibin da aka samu ya karya daya daga cikin dokokin tabbas zai fuskaci hukunci. Daga cikin wadannan dokokin, akwai dokar da ta ce ba’a yarda kowanne dalibin da shiga dakin jarabawa da wayar salula ba.
‘Akwai shi baro-baro a rubuce a cikin dokokin rubuta jarabawar makarantar, wannan dalilin ne ya sanya muka dauki matakin kona wayoyin saboda sauran daliban su gujewa aikata irin haka nan gaba,’ inji shi
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: