Connect with us

WASANNI

Mahaifin Neymar Ya Mayarwa Da PSG Martani

Published

on

Mahaifin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Neymar Snr, ya soke kungiyar da dan wasan yake wato PSG, inda ya ce sun san da cewa dan wasan zai kara kwanaki kafin ya koma kungiyar cigaba da daukar horo saboda raunin daya samu da kuma wani abu da yakeyi na taimakawa mutane a Brazil

Kungiyar kwallon kafa ta PSG dai ta fitar da wata sanarwa ranar Litinin inda take zargin dan wasan na Barzil, wanda yake son barin kungiyar da cewa yaki komawa tare da ragowar ‘yan wasan kungiyar domin cigaba da daukar hoaro.

Tun bayan kammala kakar wasan data gabata ne dai Neymar ya bayyana cewa yana son barin kungiyar domin komawa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona kuma har ya bayyana cewa bazai koma PSG din ba da daukar horo har sai sun sayar dashi.

“Mu na da harkoki na kasuwanci da mu ke yi kamar yadda kowa ya sani a karshen kakar wasa kuma kusan shekara biyar kenan munayin wannan aikin saboda haka babu wata doka da Neymar ya karya domin sun san komai,” in ji mahaifin dan wasan.

Ya cigaba da cewa “Shi kansa shugaban PSG Din yana halartar shirye shiryen da mukeyi na tallafawa marasa gata a kasar Brazil kuma yasan cewa Neymar yana da karin kwanaki saboda haka abinda sukace Messi yayi bamuji dadi ba”

Sai dai tuni shugabannin kungiyar sun bayyana cewa zasu dauki mataki akan dan wasan bayan da yaki komawa filin daukar horo domin cigaba da shirye shiryen fara kakar wasa mai zuwa da za’a fara a watan Agusta mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: