Connect with us

LABARAI

Mai A Arewa: Sai Mun Ga Abin Da Ya Ture Wa Buzu Nadi – Kyari

Published

on

Sabon Babban shugaban rukunin kamfanin kula da harkokin mai na Najeriya, NNPC, Mista Mele Kyari, a jiya Laraba ya bayyana cewa, kamfanin na NNPC zai cigaba da fafutukar nemo mai a Arewacin kasar babu-ji-babu-gani har sai ya ga abinda ya ture wa buzu nadi.

Kyari ya bayyana hakan ne a lokacin da a ka gabatar da shi ga Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, inda ya gada Mai Kanti Baru ya kai shi gaban shugaban a karo na farko da hawansa kujerar shugabancin kamfanin na NNPC a fadar gwamnatin tarayya da ke Aso Rock a Abuja.

“Za mu cigaba da neman mai a Arewacin kasar nan, da ma wasu sassan kasar,” in ji shi.

Ya cigaba da cewa, “mu na da wurare hatta a Kudancin kasar nan da har yanzun ba mu bincike su ba.

“Duk za mu bi su mu lalubo man da ke dankare a cikinsu ta yanda kowa zai amfana daga gare shi. Da yardan Allah za mu yi hakan,” in ji Mista Kyari.

A ranar Litinin ne Kyari ya amshi ragamar shugabancin kamfanin na NNPC daga hannun tsohon shugaban kamfanin Maikanti Baru, wanda ya yi ritaya bayan cika shekara 60 da haihuwa, kamar yadda dokokin kwadago na Najeriya su ka tanada.

A nan Kyari ya kuma yi alkawarin zai yi aikin nashi tare da sanya tsoron Allah a ciki.

“Na fahimci girman aikin da a ka dora ma ni; amanar da ke tattare da wannan aikin da sa ran da shugaban kasa ya ke da shi na mayar da wannan kamfanin ya zama kamfani mai takara da takwarorinsa na Duniya, ya hada har da fuskantar abinda ya shafi man fetur da iskar gas.

“Za mu himmantu wajen ganin mun sauke nauyin da a ka dora ma na a cikin mafi karancin lokacin da ya dace.

“Ina tabbatar wa da kowa cewa za mu yi wannan aikin ne tare da gaskiya da rikon amana,” in ji shi.

Ya ce za su yi aiki ne tare da hukumar EFCC da sauran hukumomin hana cin hanci da karbar rashawa, don tabbatar da tsarkake yanayin aiki tare da taya Shugaba Buhari cika alkawarin da ya daukar wa ’yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe na kawo karshen aikata almundahana a harkokin tafiyar da gwamnatin Najeriya kafin karewar wa’adin mulkinsa na karshe a 2023.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!