Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Dattawa Da Ta Wakilai Sun Sha Bamban Kan Batun Sakin El-Zakzaky

Published

on

•A Sake Shi Kafin Lamura Su Rincabe – Majalisar Wakilai

•Majalisar Dattawa Kuwa Ta Yi Tir Da Mamaye Majalisa Da ‘Yan Shi’a Suka Yi

A jiya Laraba ne majalisar wakilai ta kasar Nijeriya ta nemi gwamnatin Nijeriya da ta bi umarnin kotu wajen sakin jagoran ’yan uwa Musulmai a Nijeriya da a ka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, tun kafin lamura su kara tabarbarewa da sukurkucewa a kasar.

Majalisar ta shaida cewar hakan ne kawai zai kawo karshen rashin jituwa da a ke samu a tsakanin magoya bayansa da su ke zanga-zangar neman a sake shi kullum a babban birnin tarayya kasar, Abuja.

Sai dai a zauren Majalisar Dattawa ta kasar kuwa, ita ta bayyana cewa, bukatar da mabiya Shi’ar su ka bijiro ma ta da ita na tilasta bangaren zartarwa da ya tabbatar da cewa, an sako mu su jagoran nasu, ta zarce ikon majalisar ta dattawa.

Ita ma dai majalisar ta wakilan ta yi tir da mamaye majalisar da ’yan Shi’ar suka yi a ranar Talata wanda har hakan ya jawo rashin jituwa a tsakaninsu da jami’an tsaron da su ke gadin majalisar, lamarin dai ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Wannan matakin na zuwa ne bayan wani kudirin da shugaban marasa rinjaye na majalisar Ndudi Elumelu (PDP daga Delta) ya gabatar a kwaryar majalisar domin muhimmancin da batun ke da shi ga zaman lafiyar kasa.

Hon. Elumelu wanda ya jagoranci muhawarar a cikin majalisar ya shaida cewar tilas ne a dauki matakin da ya dace duba da kara samun rashin jituwa da tashin hankalin da ake yawan samu a sakamakon zafafan zanga-zangar neman a sake El-Zakzaky da magoya bayansa ke yi kullum a Abuja.

Mafiya yawa daga cikin ‘yan majalisar sun amince da wannan kudurin su na masu cewar tabbas da bukatar a shawo kan matsalar don kar ta wuce gona da iri, suna masu shaida cewar tabbas ci gaba da tsare El-Zakzaky wata gagarumar damace ta ci gaba da samun matsalar rashin tsaro da salwantuwar rayuka a kasar nan; kana a dalilinsu na gaba da suka bayar na neman a sake Zakzaky sune batun zaman lafiyar kasa da kwanciyar hankalinta.

’Yan majalisun sun gargadi hukumomi da cewar kada a kuskura a bari makamancin abu irin na Boko Haram ya sake barkewa a Nijeriya, “Da bukatar mu dau darasi daga baya,” A cewar ‘yan majalisar.

Dan majalisar da ke wakiltar Akwa Ibom na jam’iyyar PDP, Onofiok Luke, ya shaida cewar abun takaicin ma shine ‘yan majalisa ne ke da iko da damar yin doka da zana doka, amma gwamnatin Nijeriya tana take dokokin da akwai ta hanyar kin biyayya wa umurnin kotu na sake shugaban ‘yan Shi’ar, “Hakan na zubar wa Nijeriya da kima a idon duniya,” A cewar shi.

A cewar Luke, “Idan har Kotu za ta sake shi ta kuma bayar da umurnin a sake shi, muna kira ga gwamnati ta sake shi din. Ku sake shi, domin ba mu bukatar su sake zuwa su mamaye mana majalisar kasa kuma,” A cewar shi Hon. Luke.

Shi kuma dan majalisar dokokin Bamidele Salam (PDP, Osun) ya misalta ci gaba da tsare El-Zakzaky a matsayin rashin adalci, “Da zarar aka zalumci wani guda, to an zalumci kowa da kowa.

“Ina son na jawo hankalin gwamnatin tarayya ta duba batun jagoran ‘yan Shi’ar nan cikin gaggawa ta bi umurnin kotu don gudun kada ta jawo makamancin rikicin Boko Haram wanda rikicin ‘yan Shi’a zai ninka na Boko Haram,” A cewar shi.

Shi kuwa, Hon. Simon Dabou (APC daga Filato) cewa yake ci gaba da zare Al-Zakzaky bayan da kotu ta bada umurnin sake shi cin fuska ne wa doka da oda, don haka ne shi ma ya nemi gwamnatin ta sake shi, “A sake shi alabashi a bar jami’an tsaro su sanya ido akan harkokinsa,” A cewar shi.

Sai dai kuma fa, ita majalisar dattawan Nijeriya ta shaida cewar ba daidai ba ne ‘yan Shi’a su dauki matakin mamaye majalisar kasa, don bayyana bukatunsu. Dattawan sun shaida cewar da bukatar ‘yan Shi’ar su bi matakan da su ka dace domin samun nasarar bukatunsu.

Bugu da kari, mamba a kwamitin yada labarai na majalisar dattawan Nijeriya, Betti Apiafi, ta shaida cewar bukatun mambobin Shi’a ta zarce karfin majalisar kasa.

Ta shaida hakan ne a cikin wata kwafin sanarwar manema labarai da suka fitar hadi da aiko wa LEADERSHIP A YAU kwafin sanarwar, an hado jawabin ne a lokacin da wasu mambobin kwamitin ke ganawa da ‘yan jarida a jiya Laraba. tawagar kwamitin wanda shugaban kwamitin Adedayo Adeyeye ya shugabanta, sun yi sukar ne akan mamaye majalisar kasa da masu zanga-zangar neman a sake Shaikh Ibrahim El-Zakzaky suka yi a ranar Talata.

Magoya bayan Malamin dai suna kan gudanar da zanga-zangar tasu ne a lokacin da suka isa majalisar kasa kana daga baya lamarin ya koma tashin hankali a lokacin da suka yi kokarin shiga mashigar majalisar ta biyu.

Lamarin dai ya jawo asaran rayukan mambobin Shi’a biyu, da kuma harbin jami’an ‘yan sanda guda biyu. ‘yan sanda dai sun shaida cewar sun kame ‘yan Shi’a 40 daga cikin ‘yan shi’ar da ake zargi sun shiga zanga-zangar.

Da ya ke tir da lamarin, Mista Adeyeye ya shaida cewar masu zanga-zangar neman a sake musu shugabansu sun sha karfin jami’an tsaron da suke aiki a babban mashigar da aka fi sani da MOPOL Gate inda suka shiga cikin majalisar zuwa kofa ta biyu.

Ya tabbatar da cewar majalisar wurin kowa da kowa ne amma, “Eh majalisar kasa wuri ne na kowa da kowani kowani dan Nijeriya, amma dole ne kowani dan kasa ya bi hanyoyin da suka dace domin samun damar shiga cikin majalisar,” a cewarshi.

Ya nemi jami’an tsaro da su tabbatar da kare majalisar kasa da sauran muhallan da suka dace.

Da ya ke amsa tambayar ‘yan jarida dangane da koken da ‘yan Shi’ar suka ce sun gabatar wa majalisar, ya shaida cewar magoya bayan El-Zakzaky din sun gabatar da kokensu ne wa majalisa ta takwas amma ba wasu ba.

“Ba su gabatar da kokensu ga wannan majalisar ba a iya sanina. Kodayake, idan da za su bi wannan hanyar gabatar da koken ma da zai yi dace, su kawo kokensu ga majalisa don a san abun yi. Suna iya turo mutun guda ko biyu su nemi a basu damar tattaunawa, za mu sauraresu mu ji kokensu,” A cewar shi.

To meye sa ita majalisar kasar ba zata yi wani abu kan lamain zanga-zangar kungiyar da bukatunsu ba? Tambayar ‘yan jarida sai Misis Betti Apiafi ta amsa da cewa, “Muna kokarin shiga cikin lamarin da mutaen da abun ya shafa domin kokarin lalubo bakin zaren shawo kan matsalar. Mun yi ganawa daban-daban da majalisar wakilai ta kasa tare da kwamitin tsaro na kasa da sauran kwamititocin da abun ya shafa, ina tunanin hanyoyin da muke bi sune suka fi dacewa,” a cewarshi.

Ta ce tattaunawar tana ci gaba da gudanuwa cikin mutunta kowani bangare daga fadin kasar nan, “Suna da hakkin su yi zanga-zanga amma dai ba mu son su zo da yawa, domin zuwansu da yawa barazana ne sosai,” A fadinta.

“Mu na son a kowani lokaci suke turo wakilai ba wai su zo da yawansu ba. Idan suka turo wakilansu hakan zai bi bamu saukin saurarunsu da basu cikakken hadin kai, kana za su fi samun goyon baya daga garemu. Na sani wani hukunci daya ko biyu daga kotu akan wannan kes din,” A cewar ta.

LEADERSHIP A YAU dai ta nakalto cewar Ibrahim E-Zakzaky ya kasance a tsare ne tun shekarar 2015 bayan rashin jituwar da aka samu a tsakanin mabiyansa da jami’an tsaron da suke tawagar shugaban sojojin Nijeriya Yusuf Buratai a Zariya da ke jihar Kaduna.

Kotu dai ta ce a sake shi, inda gwamnatin tarayya a karkashin shugaba Buhari ta ki sake shi.

Wannan matakin dai ya jawo zanga-zanga masu zafi, a ranar Talata ne ‘yan Shi’ar suka je majalisar kasa da yawan gaske suna neman gwamnati ta sake musu shugabansu. Kawo yanzu dai lamarin Al-Zakzaky da magoya bayansa na kara daukan sabon salo musamma yadda ‘yan kasa ke ci gaba da furta ra’ayoyinsu daban-daban, da dama dai suna kira ga a samu yadda za a yi domin kare kasa da tsaron kasa daga kowace irin barazanar da ka iya tasowa.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: