Connect with us

LABARAI

Majalisar Malamai Ta Karrama Barden Madakin Kano

Published

on

A ranar Asabar din da ta gabata ne, Kungiyar Majalisar Malamai ta Kasa reshen Jihar Kano, karkashin jagorancin Malam Ibrahim Khalil, ta karrama Dakta Garba Baban Ladi, Barden Madakin Kano.

Ko shakka babu, akwai manya-manyan dalilai da kuma darussa da suka sa wannan Majalisa ta Kasa reshen Jihar Kano karrama Barden Madakin Kano, Dakta Garba Baban Ladi a daidai wannan lokaci.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sheik Ibrahim Khalil, a lokacin da yake yin nasa Jawabi ga dimbin al’ummar da suka halarci taron walimar da Majalisar Malaman ta Jihar Kano ta shirya wa Dakta Baban Ladin a tsohuwar Jami’ar Bayero ta Kano.

Sheik Khalil ya kara da cewa,  sun shirya wannan karramawa ne sakamakon bayar da Digirin girmamawa da Jami’ar Ibadan ta yi na karrama Mai girma Barden Madakin Kano, Dakta Garba Baban Ladi, bisa la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa na ilmantar da al’umma a sha’anin addinin Musulunci da kuma na Boko sama da shekaru 50 da suka wuce a Makarantun Manya (Adult Education), wanda dubban al’umma suka amfanu da ilmin nasa.

Shi ma a nasa jawabin, Sheik Dakta Umar Sani Fagge, Mataimakin Shugaban Majalisar Malaman na Kasa reshen Jihar Kano, ya bayyana cewa ko tantama babu  kyakyawar akida da kuma manufa ce ta baiwa Dakta Garba Baban Ladi, aiwatar da irin wadannan abubuwa na raya dan Adam, musamman ta fuskar ilmi. Domin kuwa, ana iya raya dan Adam ne kadai ta hanyar ciyar da shi da kuma ba shi iimi, amma idan ka raya shi ta bangaren ilimi, kamar ka raya al’umma ne baki daya.

Don haka, wannan karramawa da wannan Majalisa ta Malamai ta yi, babu shakka babban darasi ne ga sauran al’ummarmu baki daya. Kazalika, a koda yaushe kyakyawan aiki  shi ne ke haifar da kyakyawan sakamako, ma’ana  duk wanda ya aikata wani abin kirki na baya za su  gani kuma su  yi koyi da wannan abin kirki a matsayin darasi, a cewar Sheik Fagge.

Har ila yau, Sakataren Majalisar Malaman Reshen Kano, Malam Ibrahim Abubakar Tofa, bayyana farin cikinsa ya yi da wannan rana ta nuna wa duniya sakamakon abin kirkin da mutum ya yi, wato sakamakon kyautatawa kuma wannan wani abu ne da kowa zai yi don kansa, domin kuwa duk wanda ya yi aiki na gari,  kansa ya yi wa haka nan wanda ya yi akasi haka.

Haka nan, shi ma  Farfesa Abdalla Uba Adamu, Shugaban Jami’ar Mara Katanga (NOUN) ya bayyana namijin kokarin da Dakta Garba Baban Ladi ya yi, musamman idan aka la’akari da dubban daliban da ya koyar, inda wata majiya ta bayyana cewa, ko shekarar da ta gabata ya yaye dalibai sama da dubu70 a wannan Makaranta tasa ta manya. Daga nan ne kuma, Farfesan  ya mika wasu Jakunkuna masu daraja ga Sheik Ibrahim Khalil da kuma Dakta Garba  Baban Ladi.

A karshe, shi ma wanda aka hada taron domin shi, Dakta Garba Baban Ladi, ya  gode wa wannan Majalisar ta Malamai karkashin jagorancin Sheik Ibrahim Khalil, sakamakon wannan karramawa da aka yi masa, ya kuma nuna matukar jin dadinsa tare da mamakin yadda aka yi Malam Ibrahim Khalil din ya san shi da kyau haka. Sannan ya gode wa Farfesa Yahuza Bello, Shugaban Jami’ar Bayero da Madakin Kano da kuma sauran manyan baki, dalibai, masoya, iyalai, ‘Yan Jarida da sauran dukkanin wadanda suka taimaka wajen samun  nasarar wannan walima ta karrama shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: