Connect with us

JAKAR MAGORI

Matata Mafadaciya Ce, Cewar Wani Miji A Kotu

Published

on

Wani dan kasuda daga Ibadan mai suna Wasiu Ajibola ya bayyana wa wata kotun ‘Mapo Customari Court’ da ke Ibadan cewa, a raba aure tsakaninsa da matarsa Sadiya, wanda su ka kwashe shekara 15 tare, sakamakon fitinar matarsa da kuma rashin yi masa biyayya.

Da ya ke shaidawa alkali mai shari’a Cif Ademola Odunade, Wasiu wanda ya ke zaune a yankin Ayegun cikin garin Ibadan, ya bayyana cewa, matarsa ba ta yi masa biyayya, ita mafadaciya ce, sannan ga yawan jan sa fada. “Ya mai girma mai shari’a, na auri Sadiya ne, saboda ina tunanin za ta iya bin dokar aure sau da kafa. “Daga baya sai na fahimci cewa, ita fitinanniya ce kuma ba wanda ta ke jin maganar shi. Idan na ba ta shawara ko kuma umurnin a kan abinda ya shafe mu, sai Sadiya ta yi abinda tag a dama.

“Abin takaicin shi ne, ta na yawan ja na fada, sannan ba ta ba mu abinci da ni da yarana. “A cikin ‘yar kwanakinnan, ta kira mahaifiyarta a wayar salula, inda ta ke fada mata cewa wai na mutu. “Ina yawan ja na fada, sakamakon yawan fadan da mu ke yi, ya sa babu sauran soyayya tsanin ni da ita,” in ji Wasiu.

Da ta ke maida martani, Sadiya ta musanta dukkan zargin da mijinta ya ke yi mata. Sadiya ta yi ikirarin cewa, mijin nata ya na dukan ta. “Duk da irin kokari kulawa da shi da kuma mahaifiyarsa, amma kuma bai ya godewa,” in ji Sadiya ta bada wa kotu.

Da ya ke yanke hukunci, alkali mai shari’a Odunade ya bayyana cewa, kotu ta fahimci cewa babu sauran soyayya tsakanin Wasiu da Sadiya, domin haka, kotu ba ta da wani zabe illa ta raba aurensu. Ya bai wa Wasiu umurni daukar dawainiyar yaron da su ka haifa da Sadiya. Ya kuma bai wa Wasiu umurnin ya biya Sadiya kudi naira 5,000 a duk wata, a matsayin kudin shayar masa da yaro, sannan zai dunga daukar duk wani dawaiyiyar yaro na makaranta da sauran su.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: