Connect with us

WASANNI

Messi Ba Shi Da Tarbiyya – Alkalin Wasa

Published

on

Alkalin wasan da ya jagoranci wasan hamayyar da a ka buga tsakanin tawagar kasar Argentina da Brazil wanda Brazil ta samu nasara, Roddy Zambrano, ya mayarwa da Leonel Messi Martani inda ya ce ya yi kokari wajen ganin bai nuna san zuciya ba a wasan da aka fafata a gasar cin kofin Coppa America tsakanin Brazil da Argentina wanda Brazil ta samu nasara.

Alkawalin wasan, dan asalin kasar Ekuador shine wanda ya jagorancin wasan kusa dana karshe da aka fafata tsakanin kasashen biyu wanda kuma Brazil din ta samu nasara daci 2-0 sai dai dan wasan Barcelona, Messi, yayi zargin cewa sun samu damar bugun fanareti har sau biyu amma alkalin wasan ya hana su.

Dan wasa Dani Albes ne dai yayiwa Sergio Aguiro keta a zargin da Messi yayi na farko sai kuma dan wasa Arthur wanda shima dan Barcelona ne wanda Messi yayi zargin shima ya yiwa Nicolas Otamendi mugunta shima amma alkalin wasa ya bayyana cewa duka ba abinda yakamata a bayar da bugun fanareti bane.

“Gaba daya zargin da Messi yakeyi ba gaskiya bane saboda Albes bai yiwa Aguiro komai ba a karshe ma dana duba Aguiro ne mai laifi sannan kuma maganar Otamendi wannan zan iya cewa kowa ya yiwa kowa keta tsakaninsa da Arthur saboda haka babu wata cuta dana yiwa Argentina” in ji Roddy Zambrano, wato alkalin wasan.

Ya cigaba da cewa “Ban taba kaucewa hukuncin BAR ba saboda haka babu wani abu daya faru ba tare dana je na duba ba duk da cewa kafin a fara wasan BAR din ta samu matsala amma kuma daga baya an gyara saboda haka maganar Messi akwai rashin tarbiyya aciki”

Brazil ce dai ta lashe kofin bayan data doke kasar Peru daci 3-1 a wasan karshen da suka fafata kuma dan wasa Gabriel Jesus ne ya jefa kwallon farko a ragar Peru kafin daga baya kuma Arthur ya jefa ta biyu sai kuma dab da za’a tashi daga wasan Richarlison, dan kungiyar Eberton ya cilla kwallo ta uku da bugun fanareti sai dai tun kafin a tafi hutu rabin lokaci itama Peru ta samu kwallo daya da bugun fanareti a lokacin da wasan yake 2-0.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!