Connect with us

RAHOTANNI

Murnar Ganin Mufti Menk Ta Bar Baya Da Kura A Jami’ar Al-Kalam?

Published

on

Sanin kowa ne jami’ar Musulunci ta Al-kalam da ke Katsina sansani ne na tarbiyya da sanin ya kamata. Don haka duk wanda ya karanta labarin da wata kafar sadarwa ta yanar gizo ta yada da Hausa mai kanun ‘Daliban Jami’ar Al-kalam Sun Ba Mufti Menk Kunya’, wai sun hana shi yin karatu, zai yi mamaki da shakku, musamman ga wanda ya halarci ziyarar da mashahurin malamin ya kai.

Duk wanda ya san Bahaushe tun asali girmama bako da nuna ma sa karamci da murna wajen taryen sa ya san ya na cikin kyawawan dabi’unsa. Don haka ba zai zamo abin mamaki ba don yadda shugaban Jami’ar Farfesa Shehu Garki Ado ya tsaya tsayin-daka wajen taryen bakon cikin girmamawa duk kuwa da cewar ba hukumar jami’ar ce kai tsaye ta gayyace shi ba.

Kungiyar dalibai ta MSSN ce ta ga dacewar ya kawo wa Al-kalam ziyara kasancewar jami’ar ita ce irinta ta farko a kasar nan. An nuna a takardar gayyatar zai iya zuwa jami’ar tun karfe daya na rana zuwa hudu. Don haka dalibai na jami’ar Al-kalam da ma wasu da dama daga ko’ina cikin jihar ta Katsina su ka yi wa jami’ar tsinke tun goman safe su na dakon isowar malamin.

Nan su ka yini zungur har sai biyar saura na yamma malamin ya samu karasowa saboda yawan ziyarce-ziyarcen da ya gabatar a cikin gari. An kuwa san yadda zakuwa take da doki na wand aka ke son a gani inda a baya sai dai ka gan shi a kafar sadarwa. Murnar ganin shi tun daga nesa musamman na fitar da tsammani da suka yin a halartarsa shi ya dau hankalinsa da masu fashin baki.

A ka’ida ba a shirya zai yi wani wa’azi ko lakca ba kawai zai kawo ziyara ne a gaisa kamar yadda kuma hakan aka yi bai gabatar da kowacce irin lacca ba don ba a shirya hakan ba.Amma sai ga wata kafar yada labarai tana yada labarin kanzon kurege wai an yi ihu lokacin da yake gabatar da karatu . “Wanne karatu? Wannan kazafi ne da neman batawa daliban suna kamar yadda wani dalibi ya bayyana wanda yana cikin masu jiran zuwan malamin har kuma aka kammala yana nan.”

Ko bayan ya shigo shugaban jami’ar ta Al-kalam shi ne ya yi jawabin maraba kuma dakin taron ba wata hayaniya.

“Tabbas an yi murna watakil duk inda ya je bai sami cincirindon matasa masu kishi da dakon ganinsa kamar yadda aka yi masa dafifi a jami’ar Al-kalam ba wanda kishin addinin ne da kyakkyawan tsarin da aka dora makarantar a kai na kaunar duk wani abu da ya shafi addinin Musulunci .

“Rashin sanin al’adunmu da dabi’unmu da yadda muke taryen bakinmu mu ke nuna murna da karramawa da annushuwa a idonsu don nuna kauna watakil shi ya sa har Mufti Menk ya yi wancan furucin.

“Sannan ma ai ko ina Mufti ya je a duniya in har zai je jami’a ne kuma gun matasa masu irin wannan shekarun irin wannan taryen za a yi masa don nuna murnar ganinsa kada ya manta fa ba hukumar makaranta ce ta gayyace shi ba wadannan yaran ne.

“Don haka ba wani abu ba ne sabo da har Mufti zai yi irin wannan magana ta nuna rashin jin dadi kawai dai an yi masa uziri ne saboda akwai gajiya a tare da shi .Amma daliban jami’ar sun nuna dattaku da tarbiyya don kuwa ba wanda ya tashi daga wajensa ko don daukar hoto ko gaisawa da shi ko tare masa hanya,” ta bakin wasu dalibai da suka yi ruwa da tsaki wajen tabbatar da zuwansa jami’ar.

An yi taro an kammala lafiya daliban jami’ar Al-kalam sun ba shi kyautar girmamawa ya amsa cikin farin ciki da godiya sannan a karshe ya yi musu alkawarin kuma dawo wa jami’ar duk lokacin da ya kuma zuwa kasar da yardar Allah. Mahalarta taron sun jnjina tare da fatan alheri ga jami’ar ta Al-kalam na ci gaba da rike kambunta na jami’a ta farko a kasar nan wadda ta zama ba ilimi kadai ake koya a cikinta ba har da tarbiyya ta zahiri da badini. Amin.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: