Connect with us

LABARAI

Na Shiga Kungiyar Asiri Ne Don Na Kare Kaina, Cewar Wani Dalibi

Published

on

Wani dalibin karamar makarantar Sakandare mai suna, Christopher Anthony, mai shekaru 14 da haihuwa a duniya, ya amsa cewa, ya shiga kungiyar asiri ne domin ya yaki wasu makiyansa, ya kuma kare kansa daga masu zaluntarsa a makaranta.

Matashin yaron ya ce, yana zaune ne a kauyan, One-Man Billage da ke karamar hukumar Karu, ta Jihar Nasarawa.

Ya amsa aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa a lokacin da ‘yan sanda suka gabatar da shi a gaban manema labarai a Lafiya, hedikwatar Jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar, Mista Bola Longe ya ce, “Ina yin kira ga iyaye da masu kula da yara da su cika aikinsu a matsayinsu na iyaye ta hanyar baiwa yaran na su tarbiyar da ta dace, su rika kula da kai-komon yaran na su, musamman wadanda suke a makarantun Sakandare da sauran manyan makarantun Jihar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: