Connect with us

LABARAI

NAHCON: Jihar Kano Ce Ta fi Sauran Jihohi Ingantaccen Tsarin Aikin Hajji

Published

on

•Za Mu Gina Masaukin Alhazai A Kano Mai Daukar Alhazai 500 – Shugaban Hukumar

Shugaban Hukumar Alhazai na Kasa, Barista Abdullahi Mukhtar ya bayyana jihar Kano a matsayin  wadda ta dara sauran Jihohin Kasar nan a bangaren batun tsari da kuma bin doka a yayin aikin Hajji, “ina matukar fari tare da alfaharin cewa,  Hukumar Alhazan Jihar Kano ce ke kan sahun gaba wajen gudanar da ayyukan alhazai musamman ta fuskar bin doka da kuma da aka shinfida wa Mahajjatan.”

Baristan ya bayyana haka ne, a lokacin da ya jagoranci Jami’an Hukumar Alhazan ta kasa domin ziyartar Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Fadar Gwamnatin Kanon. Har ila yau, ya kara da cewa, sun ziyarci Fadar Gwamnatin Kanon ne domin duba tsare-tsaren da Hukumar Alhazan Jihar Kanon ke kai don tunkarar aikin Hajjin na bana. Kazalika, Hukumar jin dadin Alhazan Jihar Kanon, har yanzu tana nan a kan wannan kyakkyawan shiri da kuma tsare-tsare wanda ta samu nasara a kan horarwa ta musamman wadda Hukumar Alhazai ta Kasar Sudiyya ta tsara da kuma Hukumar Alhazan tan an Nijeirya.

Haka zalika, Shugaban ya ci gaba da cewa, mun gamsu kwarai da gaske musamman ta fuskar tsare-tsaren wayar da kai da Hukumar Alhazan Jihar Kano ke gudanarwa don ilmantar da Maniyyata muhimmancin ayyukan  Hajji.  Wakazalika, a bangaren aikace-aikace daga nan gida Nijeriya zuwa Kasa mai tsarki, Jami’an Alhazan Jihar Kanon na yin iya bakin kokarinsu don samar da kyakkyawan yanayin da ya shafi harkokin lafiya tare da tabbatar da walwalar Mahajjatan nasu, in ji shi.

Dangane da kokarin Hukumar Alhazan ta Kano, Barista Abdullahi Muktar  ya sake bayyana cewa, nan ba da jimawa ba tawagar Hukumar Alhazan ta kasa za ta dawowa Jihar ta Kano, domin kaddamar da ginin  masaukan Alhazan wanda ake sa ran zai dauki akalla mutane 500 wanda za a gina a Jihar Kanon.

Babu shakka, wadannan Masaukai an tsara su ne ta yadda za su dauki akalla mutane 500, fatan mu a nan shi ne, da zarar an kammala wannan aiki,  da yardarm Allah Maniyyata sun daina kwana  a sansanin Alhazai kafin tashinsu zuwa kasa Mai tsarki (Saudiyya). Daga nan kuma, Barsitan ya sanar da Gwamna Ganduje  cewa, tuni an fara aikin gina cibiyar lafiya a sansanin Alhzan ta Kano, a matsayin Asibitin da Mahajjatan za su cigaba da amfani da shi da kuma sauran al’ummar Jihar Baki daya.

Da ya ke karbar Shugaban Hukumar Alhazan ta Kasa , Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda Mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna, ya wakilta, ya bayyana matukar farin cikinsa ga Shugaban Hukumar Alhazan ta kasa, bisa samar da dukkanin tallafin da ake da ya shafi harkokin ayyukan Hajji.

Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa, zan yi amfani da wannan dama domin bayyana gamsuwarmu tare da godiya ga daukacin Jami’an Hukumar Alhazai ta Kasa bisa samar da tallafi a kan lokaci dangane da dukkanin wata bukata da Jihar Kano ta gabatar a gabanta, ko shakka babu, ana kula da Kano kwarai da gaske wajen ba ta kujeru masu dama da kuma samar mata da wadataccen lokaci na tashin Alhazai da sauran makamantansu, in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, tuni shirye-shirye sun kusa kammala na fara tashin Alhazan Jihar Kano na wannan shekara, wanda a ke fatan farawa a ranar 12 ga watan da mu ke ciki da yardar Allah.

Kazalika, watanni shida da suka gabata Jihar Kano ta karkashin Hukumar jin dadin Alhazai ta fara gudanar da bitocin karawa juna sani  da kuma harkokin wayar da kai ta kafafen yada labarai a cibiyoyi 32 da ke fadin Jihar Kano.

Saboda Haka, Gwamna Ganduje ya tabbatar da cewa Gwamnatinsa za ta cigaba da bayar da dukkanin goyon bayan da a ke bukata, musamman a irin wannan lokaci da Hukumar jin dadin Alhazan ke bujiro da sabbin fasashohi domin inganta harkokin aikin Hajjin, kamar yadda Sakataren Yada Labaran Mataimakin Gwamna, Hassan Musa Fagge, ya Shaida wa LEADERSHIP A YAU.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!