Connect with us

LABARAI

Ranar Yawan Al’umma Ta Duniya: ’Yan Najeriya Sun Kai Kimanin Milyan 198

Published

on

A ranar Laraba ce, daraktan hukumar kididdigar yawan al’umma ta kasa, Dakta Ghaji Bello, ya ce hukumar na shi za ta yi amfani da hanyar kimiyyar zamani wajen tantance ainihin yawan al’ummar Nijeriya. Bello ya ce, a halin yanzun dai Nijeriya tana kiyasta yawan al’ummarta ne a kan milyan 198, ya kara da cewa, amma hukumar ta kuduri aniyar tabbatar da kidayar ta gaskiya abar dogaro a nan gaba.

Babban daraktan yana wannan maganan ne tare da kamfanin dillancin labarai na kasa, a Abuja, ranar Alhamis, a bisa shirye-shiryen tarbar ranar kididdigan yawan al’umma ta Duniya.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiwa hukumar goyon baya a kan shirin da take yi na gudanar da ingantaccen lissafin yawan al’ummar kasar nan.

“Mun tsaya ne a bisa kiyasin yawan al’ummarmu a kan milyan 198 bayan da muka tsame duk abin da ya shafi mace-mace da makamantan hakan,” in ji shi. A cewar shi, hukumar za ta dauki hotunan yatsun mutane a lokacin kidaya na gaba ta hanyar yin amfani da mashinan da za su iya gano duk wanda ya dangwala yatsarsa sau biyu.

Daraktan ya bayyana cewa, tun da jimawa ne ya kamata a gudanar da kidayan jama’an, shekaru 10 bayan da aka gudanar da wancan kidayar a kasar nan. Bello ya bayyana tabbacin da yake da shi na cewa hukumar na shi za ta iya gudanar da kidayan na gaskiya, ya yi kira ga gwamnati da ta amine da hakan.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya kawo rahoton da ke nuna cewa, a ranar Alhamis mai zuwa ne za a gabatar da bikin ranar yawan al’umma ta Duniya na wannan shekarar ta 2019, a Abuja.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: