Connect with us

KASUWANCI

Sarrafa Sukari Da Na’urar Zamani Za Ta Habaka Fannin, In Ji NSDC

Published

on

Babban Sakataren Hukumar  sanya ido akan yadda ake Sarrafa Sikari ta kasa NSDC Dakta Latif Busari, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki dake da masana’antar sarrfa Sikari dake kasar nan, dasu rungumi yin amfani da na’urar zamani waje sarrafa Sikari.

Dakta Latif Busari, ya yi kiran be a lokacin da yake jawabinsa a ranar Talatar data wuce a jihar Legas a taro karo na farko da hukumar da kuma BMA suka gudanar akan yin amfani da na’urar zamani son sarrafa Sikari a kasar nan.

Ya yi nuni da cewa, yin amfani da na’urar bawai kawai tana inganta yadda make sarrafa Sikari bane harda inganta yadda ake shi.

Dakta Latif ya danganta yin amfani da na’urar a matsayin ginshiki wajen sarrafa Sikari Inda ya jaddada cewar, akwai bukatar masu masana’antun su rungumi yin amfani da na’urar ta hanyar ware wane kason kudinsu don mallakar na’urar yadda zata kara habaka Sikarin da suke sarrafawa a kasar nan.

Ya bayyana cewar, hukumarsa a shirye take wajen ganin ta bawa masu masana’antun dukkan goyon bayan da ya dace don su mallaki na’urar yadda zasu dinga gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A cewarsa, “babbar manufar mu a matsayin hukumar gwamnati itace, mu sanya ido akan masana’antun na sarrafa Sikari yadda za’a ciyar da fannin gaba a kasar nan za kuma muci gaba da yin iya kokarin my wajen Kawo na’urar don mu bawa masu zuba jari a tannin damar yadda zasu sarrafa Sikarinsu da na’urar.”

Shi kuwa wani mai yin na’urar ta Sikari Mista Landry Maffo Melli  ya ce, yin amfani da na’urar tana Habana sana’ar sarrafa Sikari kuma tanada gwanin dadi wajen yin amfani da ita.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!