Connect with us

LABARAI

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Karin Haske Kan Nadin Sabbin Ministocin Buhari

Published

on

A ranar Laraba ne Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya shaida wa takwarorinsa a majalisar cewa, akwai yiwuwar majalisar ta karbi sunayen sababbin ministocin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke da nufin nadawa kafin karewar wannan makon.

Lawan, wanda ya ke magana a wajen zaman majalisar bayan batun da Sanata Albert Bassey Akpan (dan PDP daga jihar Akwa Ibom) ya taso da shi, inda Lawan ya ce, fadar shugaban kasar ta na yin matukar kokari a kan sunayen sababbin ministocin.

A maganar da Akpan ya tayar a majalisar ya na cewa ne, akwai bukatar shugaban kasar ya hanzarta aiko da sunayen ministocin nashi, domin majalisar ta na gab da shiga hutunta na shekara.

Amma sai Lawan ya yi nuni da cewa, a bisa abin da su ka tattauana da wasu manyan jami’an gwamnatin, akwai yiwuwar za a aiko da sunayen ministocin kafin karshen wannnan makon.

Shugaban Majalisar Dattawan ya ce, sanatocin kuma a shirye su ke da su jira  zuwan sunayen ministocin da zarar an aiko da su zuwa ga majalisar.

A makon da ya gabata ne dai wata kafar yada labarai ta bayar da labarin cewa, hukumar binciken sirri ta kasa ta farin kaya, DSS, ta kammala tantance sunayen wasu mutane 21 da a ke son a nada su mukamin ministoci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!