Connect with us

TARIHI

Tafiya Zuwa Sararin Samaniya: Abinda Zai Yiwu Da Abinda Ba Zai Yiwu Ba (2)

Published

on

Assalamu Alaikum!

A baya na kawo bayanin da shahararren masanin nan Edward Tellar ya yi a kan tafiya izuwa sararin samaniya a cikin shekarar 1961, inda a bayanin nasa ya ke fadar burin da a ke son cimmawa idan an fara zuwa sararin samaniya, don haka ga karashen bayanin nasa da cewa, abinda za mu iya shi ne mu tura haske wanda zai dauko ma na bayanai. Na san zai yi wahala hasken ya kauce daga inda a ka aike shi matsawar an tura shi, don haka zai yi ta tafiya har tsawon shekaru, a karshe za mu iya samun kallon Tauraruwa Prodima, sai dai idan a ka yi rashin sa’a cewa babu duniyoyin da a ke rayuwa a can, shin za mu tura su gaba ne? Kun ga wannan zai zamar mana aiki mai wahala kuma mai cin rai.

Alal misali, shin dukkan mutanen da ke rayuwa a sauran duniyoyin da ke fadin madaukakiyar duniya (uniberse), su ma su na bincike ne kamar yadda mu ke yi a nan? Kuma shin a sauran galakzin da ke fadin madaukakiyar duniya da akwai hadari mai kunshe da kura irin na duniyar galakzinmu, wanda ya yi ma na rumfa daga ganin cikin galakzi namu? Don haka da akwai kunson taurari a cikin gefan galakzinmu, inda taurarin ke da kusanci da juna yadda har za a samun mutanen duniyoyin su na tura sakonni a junansu da kasuwanci  kuma har za a iya samun yaki a tsakaninsu (tsakanin duniyar wannan tauraruwa da ta waccan tauraruwa).

Idan kuwa duk wannan hasashen ya kasance gaskiya, to kuwa zuwan mu can ya na da matukar hadari, domin nisan da ke tsakanin duniyarmu da taurarin tsakiyar Galakzinmu, nisa ne wanda idan a ka tura haske zuwa can duk gudunsa a sararin samaniya sai ya shafe shekaru dubu talatin sannan zai isa. Sai dai za mu iya zuwa duniyar waje inda za mu samu dammar sauraren signa ta rediyo daga duniyoyin (radio signal) ta hanyar sauraren (wabelength) nasu za mu iya fahimtar me suke fadawa junansu, daga nan sai mu san makama.

Na san wasu za su yi mamaki sarai daga cikinku a kan cewa don me mu ke ta jajircewa don ganin sai mun je tsakiyar galakzinmu ba, ma ko yin kokarin tafiya zuwa galakzi  mafi kusanci da galakzinmu mai suna Andromeda Galakzi? Ita kuwa kun sani idan a ka tura haske daga nan duniyar izuwa can sai ya shafe kimanin shekaru miliyan biyu kafin ya isa can, ga shi kuma Eisteen yace ba zamu iya tafiya da gudu ba dai-dai ko fiye da gudun haske. Ni da kaina Ina son na yi tunanin ta hanyar da za a je can domin ko shi Eisteen ya yi hasashen za a iya zuwa.

Na san babu wanda zai iya tafiya da gudu fiye da gudun haske, amma idan har injiniyoyin mu za su cigaba da yin aiki tukuru har su samar ma na da abin hawa na kwarai, lallai za mu iya yin gudu a sararin samaniya da sauri fiye da gudun haske, sai dai na iyakance cewa hakan ba zai faru ba ina raye, a hasashe na koda hakan zai faru sai nan da shekaru dari biyar masu zuwa, Ina ganin a wannan lokacin duk abin da a ka gaza yin sa a wannan duniyar a yanzu to a wannan lokacin za’a iya aiwatar dashi. Saboda haka nan da shekaru dari biyar  masu zuwa (shekara ta 2461), za’a samu wadanda za su iya zuwa Galakzin Andromeda ba ma Tauraruwa Prodima ba.

Sai dai Wani misalin kuma da nake so a duba, yanzu ace nayi tafiya fiye da gudun haskea sararin samaniya, me kuke tunani ku masu kallo daga nan duniyar zaku gani? Za ku ringa kallo nane na nufi Andromeda da tsananin gudu wanda yafi gudun haske yadda zan dauki lokaci dan kankane wajen zuwa. Shekarun tafiyar haske izuwa can yana daukarsa shekaru miliyan biyu ne da ‘yan kadan ne, idan zamuyi lissafi, lokaci (T) ya zamo shekaru miliyan biyu kenan, sai kuma nisan da ke tsakaninmu da Andromeda  (R) a daya bangaren wanda zai zamo nisan tafiyar haske a shekaru miliyan biyu kenan, sai kuma nisan da haske zai iya ci a irin wannan lokacin (shekaru miliyan biyu) (ct) wanda shima zai zamo nisan haske shekaru miliyan biyu dadan wani abu.

Idan a ka yi amfani da wadannan abubuwan wajen lissafa bambamcin lokacin da za a ci a sararin samaniya da yadda zai koma a duniyar mu, za’aga lokacin  ya koma dan kadan: (ct)^2-R^2=K (K shine sabon lokacin da za a dauka) wannan ne abinda ku da ke nan duniyar ‘earth’ za ku gani, amma ni kuma da na tafi fa?

A wurina dana hau Rocket zan zamo kamar wanda yah au jirgin sama ne daga wata jiha izuwa wata jiha, kamar yadda kuka lissafa kukaga lokacin ya kankance muku haka nima zan ga lokacin ya kankance hasalima ku lokacin a gurinku shekaru miliyan biyu ne, amma ni a gurina da na tafi zai iya zamowa shekaru ashirin.

To shikenan ma, a ce shekaru ashirin zan je Andromeda, sai dai idan na je zan iya fuskantar matsaloli da dama, daga ciki sune abinda yake a galakzin mu mai kyaune a wani galakzin fa zai iya kasancewa abu mai matukar hadari, domin babu mamaki abincin da na tafi da shi daga nan idan na je can ya zamo guba mai hatsari.

Saboda haka ma ace naje Andromeda lafiya, na zauna acan tsawon shekaru goma ina zagayawa ina bincike duk lafiya, sannan na ninko na dawo gida a wasu shekaru ashirin din duk ace na dawo lafiya. Kunga zaku iya ganin idan na dawo New york gari na, na rabu da ita ne shekaru hamsin a sararin sama, amma shekarun da duniya tayi zai zamo kwatankwacin shekaru miliyan hudu, kunga duniya ta tsufa kenan da yawa.

Duk abokaina sun mutu, babu wanda zai iya yin Magana day arena Turanci ne ko Hungarian, malaman wannan lokacin zasu rinka kallona ne da wani irin yanayi, ga shi ba za su iya karanta bayani naba tunda kun sani da turanci zan rubuta, su kuma ba su san Turancin ba, ga shi ko a yanzu Ina da shekaru Hamsin, idan na kara wasu Hamsin din a wannan yanayin ya ku ke ganin zan koma? Na san daga karshe ma gidan ajiye namun daji (zoo) mutanen wannan lokacin za su kai ni, na zama abin kallo a gare su..!

Edward Tellar ya yi wannan bayanin ne da shekaru takwas, mutum na farko ya dira a duniyar wata. Abu na gaba bai wuce makaranta su ji halin kimiya a yanzu ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: