Connect with us

KASASHEN WAJE

Takaddar Kudin ECO Za Ta Kankama A Shekarar 2020 – Ouattara

Published

on

Shugaban Kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya ce Kasashen da ke Afirka ta Yamma da suka cika sharadodin samar da kudin bai daya da aka yi wa suna ECO za su aiwatar da shirin a shekara mai zuwa ta 2020.

Shirin samar da kudin bai dayan ya samo assali shekaru sama da 30 da suka gabata, amma aka kasa samun biyan bukata saboda banbance-babancen da ke tsakanin Kasashen kungiyar ECOWAS.

A watan jiya Shugabannin su ka amince da shirin, yayin da Shugaba Ouattara ya ce Cote d’Ivoire na goyan bayansa dari bisa dari. Ana sa ran tsarin kudin ya taka muhimmiyar rawa wajen hade kan Kasashen baya ga bunkasa tattalin arzikinsu da kuma samar da ayyukan yi.

Kasashen na yammacin Afrika dai yayin taron Kungiyar AU na tsakiyar shekara da ya gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, sun amince da sanyawa kudin suna ECO wanda zai zamo takaddar kudin da ilahirin Kasashen yammacin na Afrika za su rika amfani da shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: