Connect with us

TATTAUNAWA

Tun A Wajen Neman Aure Ake Barin Tarbiyya – Abba Kagara

Published

on

ALHAJI ABDULLAHI ABBA KAGARA matashi ne mai kananan shekaru, shi ne kuma shugaban kamfanin nan na saye da sayarwa gami da al’amuran yau da kullum da su ka shafi cinikayya mai suna ‘Abba 2 World Wide Limited’  har ila yau shi ne  shugaban kungiyar nan ta tallafawa marayu, wacce ake kira da ‘Orphans Around The World’, sannan basaraken gargajiya ta Barajen Hakimin Kagara.

A wannan zantawar da ya yi da manema labarai ciki har da LEADERSHIP A YAU a ofishinsa da ke Kaduna, ya yi magana ne a kan tarbiya da kuma hanyoyin da ya kamata matasa su bi, domin taimakon kansu da kansu. Wakilinmu, UMAR A HUNKUYI, ne ya saurara, ya kuma rubuta ma na. A sha karatu lafiya:

Me ya lalata tarbiyar al’umma a halin yanzun?

Assalamu Alaikum, Batun tabarbarewar tarbiya idan muka kalle shi ta fuskacin Addini, za mu ga cewa, tun daga tsarin da akan bi a wajen neman aure yana daga cikin abin da yakan bata tarbiyan yara. Idan za ka nemi aure, matukar ka sabawa yanda Addinin Musulunci ya yi umurni da ka nemi auren, tabbas ko ka yi auren, da duk ka haifi yara tilas ne ka taras da gurbacewar tarbiyansu.

Abu na biyu kuma shine daga bangaren neman halal dinmu, in har ya kasance ba ka neman halal, kana hada dukiyarka da haram ne, to a gaskiya babu yanda za a yi danka ya sami tarbiya mai kyau kamar yanda kake so ya samu. Allah Madaukakin Sarki Ya ce mana. “Dukkanin zuriyar da aka gina ta da haramun, ba za ta yi albarka ba, sannan kuma za ta kasance mai bijirewa iyayenta ne, za ta zama annoba kuma a cikin al’umma.” Wannan kuma shi ne zahirin gaskiya.

Bai Kamata Mu Dora Laifin Lalacewar Tarbiya A Kan Matasa Kadai Ba

Ba kuma za mu ce matasa sune kadai Ummul haba’isun lalacewar tarbiya ba kadai. Ummul haba’isun lalacewar tarbiya a halin yanzun su ne iyayen matasan. Domin idan za ka fara neman Aure a Addinin Musulunci to ya kamata ne ka bi bisa ka’idojin da Addinin Musuluncin ya tanada maka, akwai tabbacin idan ka yi hakan, za ka sami saukin al’amurra. Na biyu kuma a duk inda kake neman kudi, ka tabbatar da ka rike gaskiya ta yanda za ka ciyar da iyalanka da halas, domin in ka kuskura ka ciyar da su da haramun, tabbas duk yaron da ka Haifa da haramun ya taso tilas ne sai ya zama marashin tarbiya tagari, wannan ita ce gaskiyar magana.  Don haka, ka ga a nan babu laifin matasa a gaskiya, sannan idan ka cika wadannan sharuddan biyu, sai kuma ka mayar da hankali wajen ba su ingantaccen ilimi, ilimin Addini da na zamani, kowanne kar a barshi.

Hanyoyi da ya kamata a bi wajen gyarawa ko dawo da tarbiyar al’umma kamar yanda take a can baya?

Maganar a ce tarbiyar al’umma ta koma kamar yanda take a can baya, babu abin da za a ce ba zai iya yiwuwa ba, amma abu ne mai kamar da wahala, saboda irin tsarin da muka daukarwa kanmu, a yanzun za ka ga kana makwabtaka ne da mutum amma ba ka sanshi ba, bai sanka ba, kowa yana rayuwar kanshi ne. Irin wannan rayuwar tana taba al’adar Hausawa, tana ma taba Addininmu, kamar yanda Ma’aikin Allah (S) ya yi magana a kan hakkin makwabtaka, a inda yake cewa, da a ce wani zai iya gadon wani ba tare da dalili na jini ba, to da makwabci ya gaji makwabcinsa, saboda mahimmancin makwabtakan. Don haka, wannan sakacin da ake yi a wajen makwabtaka yana sabawa Addini, yana kuma bayar da damar rashin kwabawa yaran da ba naka ba.

Mece ce shawararka ga matasa?

Shawara ta ga matasa ita ce, misali ni dai matashi ne, kuma ala ayyi halin duk abin da matashi zai yi, ya tabbatar da ya rike gaskiya, mu tashi mu nemi na kanmu, kar ka ce ka gama makaranta amma ka tsaya kana neman aiki, kar matashi ya raina karamar sana’a, mu tashi mu kama sana’a. Matasa muna fa da dama kwarai da gaske, musamman matasanmu na nan arewa, muna da dama amma ba ma amfani da ita, mun mayar da kanmu tamkar wadanda ba su san ciwon kansu ba, mun tsaya muna jiran a ba mu. Duk matashin da Allah Ya nufa da kammala karatunsa, ya tsaya ya ga wace irin karamar sana’a ce zai iya kamawa, wacce za ta taimake shi ya zama mai dogaro da kansa.

Shawarata ga iyaye fa?

Shawarata ga iyayen matasa kuwa, su tsaya su lura da rayuwar matashi tun yana dan shekara 10 zuwa 11, iyaye su lura da me ‘ya’yansu suke sha’awar su zama a irin wannan lokacin, duk abin da ‘ya’yan nan na su suke son su zama matukar dai ba abu ne da ya sabawa shari’a ba, to kamata ya yi iyaye su ba su goyon baya da gudummawa, domin ganin wannan mafarkin na ‘ya’yensu ya tabbata. In har ka taimaki danka a irin wannan lokacin ina tabbatar maka ba za ka ga dannan naka ya lalace ba.

Shawarata ga gwamnati kuma fa?

Gwamnati kuwa ita ce ma take da mahimmiyar rawar da ya kamata ta taka. Misali ni yanzun da nake yin sana’ata, matashi ne mai kananan shekaru, amma in ka lura babu wani abu na gwamnati da yake shigo mani. to idan har a ce gwamnati za ta rika duba ire-irenmu matasa da suke da zimmar yin kasuwanci da sauaran sana’o’i tana taimaka masu, ba dole sai taimako na kudi ba, a ma ba ka tsaro da goyon baya a wajen aiki ko sana’arka shi ma taimako ne. Misali ni yanzun ina kasuwa, amma ina fuskantar kalubale masu yawa, wadanda kuma ba na kudi ne ba. ka ga da farko akwai kalubale a kan batun tsaron dukiyar ma da nake yi, wanda yakan cinye akalla kashi 30 na duk wata ribar da na ke samu.

Na biyu, wajen tsawwalawa da karban haraji, a tsakani da Allah sam wannan ba taimakon ‘yan kasuwa ake yi ba, ka ga yanzun za ka ga na yi kasuwa na sami ribar naira dubu goma misali, amma a ciki na biya harajin  naira dubu hudu a misali, a cikin dubu goman nan, ma’ana na biya kashi 40. Sannan a sauran kashi 60 din nan ne zan biya ma’aikatana albashinsu da dai makamantan hakan, wanda a karshe sai ka taras babu wata takamaiman ribar da na samu.

Don haka, a nan ina yin kira ga gwamnati da mu ji tsoron Allah, kuma mu tsaya mu kyautatawa wannan kasa tamu ta gado. Idan har za mu tsaya mu taimakawa matasa kamar yanda shugabannin baya su ka yi, ina tabbatar ma ka a Nijeriya za mu fi yanda muke a halin yanzun nesa ba kusa ba wajen habaka da kuma ci gaban kasarmu gami da kyautatuwar tattalin arzikin kasarmu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: