Connect with us

LABARAI

Wata Mata Mai Ciki Da Mutum Biyu Sun Mutu Sakamakon Ambaliyar Ruwa A Filato

Published

on

Wata mata mai ciki da wasu mutum biyu sun rasa ransu sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a mutum biyu a garin Zinariya dake Jos a nihar Filato.
Kamfanin dillacin labarai na kasa ya rawaito cewa ambaliyar ruwa ta auku ne sakamakon kwana hudu da aka kwashe na yi wanda yayi sanadin rushewar gidaje tara.
Sani Bello, dan uwa ga mamatan ya bayyana wa manema labarai a ranar alhamis cewa ‘Lamarin ya auku ce sakamakon rashin magudanun ruwa masu zurfi, wanda hakan yasa ginin da sukw ciki ya rushe a kan su.
‘Yayata wadda ke dauke da ciki ta kawo mana ziyara da garin Naraguta na daga cikin wadanda ruwan yayi awan gaba da su.’
‘Mun samo gawar ta kuma mun binne ta. Har ila yau akwai wata mata da kafarta ta karye wadda a halin yanzu tana kwance a asibiti.’
Ya kara da cewa, wani yaro mai suna suna Ibrahim mai shekaru bakwai a duniya shima ya samu rauni inda shima aka garzaya da shi asibiti,’ inji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: