Connect with us

LABARAI

Yadda Taron Concert Na ABU Staff School Ya Yi Armashi

Published

on

A cikin makon da ya gabace mu ne makarantar yara ta ABU Staff School da ke a harabar jami’ar ta gudanar da bukin ranar wasa da tuna al’adun gargajiya da muke dasu a kasar najeriya bakidaya.

Wakilinmu ya sami halartar bikin ga kadan daga cikin tsarabar da ya aiko mana dashi daga wannan waje.

Bayan bude taro da addu’a sai aka buga taken Nijeriya dalubai suka gudanar da fatetin makaranta.

Bayan haka sai mataimakin shugaban makaranta Malam Umar Bala ya yi jawabin barka da zuwa ga iyaye da sauran manyan bakin da su ka sami halartar wannan taro.

Daliban makarantar tun daga aji daya zuwa shida ko wani aji ya gabatar da basirar da ya ke da shi a gaban iyaye.

Aji daya sun gudanar da mukalace da sukaiwa lakabi a turance Poem My Future.

Sai aji biyu suka gabatar da nasu da suka kirashi a turance Poem Dont gibe up.

Sai aji uku nasu basirar da suka nuna a cikin wasa sun kirashine da Poem I found out that my self

Haka nan sukaita kawo ilmi cikin wasa da nishadi ana masu tafi suna jin dadi majan baki da jinjina ga daluban da malamansu.

Dalubai masu koyan harshen French suma ba a barsu a bayaba suma sun nuna bajintarsu.

Bayan duk an tabo fannin ilmi  da lafiya da tsaro da kasuwanci a cikin wasan kwaikwsyo sai aka koma wajan rawan gargajiya da ya hada kabilun daban daban kamar su.

Hausa fulani da yarbawa da Ibo da Tibi kowace kabila tazo ta nuna bajintar su a gaban mayan baki sukuma manyan baki da suka hada da iyayen dalubai da kuma wanda makarantar suka gaiyata duk haka akaita nuna murda da shiga sabuwar shekara gama aji zuwa aji.

Bayan kammala wasanne wakilinmu yaji ta bakin shugaban kungiyar iyayen makarsntar PTA malam Muhammad Rabi’u Muhammad,akan ko me zaice game da taron? Sai ya kada baki yace taro yayi kyau kuma kullun ana samun ci gaba don na bana yafi na bara don hakama yayi kira ga iyaye da du kara kaimi wajan turo yara makarsnta don samun ci gaban karstumsu kuma yayi fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Shima shugan makarantar malam Muhamman Sani Muhammad a nasa jawabin yayi fatan Allah ya sakawa dukkan wanda suka bada lokacinsu wajan gudanar da shi taron daga malamai har iyaye karshe yayi kira ga iyaye da su kara dagewa wajan turo yara makaranta tare da sa masu idanu a kowani lokaci don karesu daga muguwar tarbiya yayi godiya ga bakin duk da suka sami zuwa taron.

An fara lafiya an tashi lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: