Connect with us

TATTAUNAWA

Yakamata Manyan Arewa Su Sa Baki Kan Sha’anin Sambo Dasuki – Usaini Mairiga

Published

on

ALHAJI USAINI ISAH MAIRIGA dan siyasa ne a jam’iyyar APC, haka zalika mai gwagwarmaya da fashin baki a duk lokacin da su ka hango wani na faruwa wanda ba su amince da shi ba, ko dai a fannin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa. A wannan tattaunawa da LEADERSHIP A YAU, Mairiga ya yi fashin baki game da tafiyar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, jam’iyyarsu ta APC da kuma cigaba da tsare da Kanar Sambo Dasuki da a ke yi. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Ya ka ke kallon zubin gwamnatin Buhari a zango na biyu?

To, kai tsaye yanzu ba za a iya yi doguwar magana ko fashin baki game da gwamnatinmu ta APC karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ba, domin a tsari irin na dimukradiyya, mulki ba na mutum daya bane, dole akwai wasu mukamai da ake bukatar samarwa domin gudanar da aiki yadda ya kamata. Yau mun shiga wata na biyu da rantsar da sabuwar gwamnati, Shugaban kasa har yanzu bai tura sunayen Ministoci ba, ashe kenan ba za a iya sanin inda salon mulkin zai sa gaba ba. Saboda haka, sai mun ga wadanda aka nada tukun za mu iya yin fashin baki a kai.

Sai dai, hakan zai hana mu janyo hankali kan rashin alfanun da ke tattare da jinkirin da ake samu wajen nada Ministocin ba. Ya kamata a ce tun kafin rantsar da shi, Shugaba Buhari ya san irin mutanen da suka dace da komawa kujerarsu da kuma wadanda za a sauya. Kowa ya san wadanda suka cancanta da wadanda ba su cancanta ba. Batu ne ake yi na aiki, saboda haka an san rawar da kowanne dan jam’iyya ya taka da kuma sakayyar da ya dace a yi masa.

Magana ta gaskiya, a ra’ayina, Buhari ba shi da wata hujja ta ci gaba da boye sunayen mukarraban gwamnatinsa ba tare da ya tura su gaban Majalisar domin tantancewa ba.

Wadanne irin mutane kake ganin ya kamata a bawa mukaman?

Wadanda suka wahaltawa jam’iyya ta fuskar cin zabe sannan ya kasance za su iya yin aikin da aka ba su. Domin akwai wadanda za ka ga sun yi kokari sosai wajen yakin neman zabe, amma idan an ba su mukami sai ka rasa ina basirarsu take. Ba za mu yi fatan ganin mukarraban gwamnatin irin na shekarun hudu da suka wuce ba. Kowa ya san irin kukan da ‘yan Najeriya suka rika yi, abubuwa da yawa ba su tafi yadda kamata ba; yaki da cin hanci rashawa ba yadda muke tsammani ba, tattalin arziki haka, zamantakewa, hatta sha’anin tsaro kara dagulewa lamura suke yi. Babu wanda ya zaci a gwamnati Buhari sace-sacen mutane da hare-hare Zamfara, Katsina da wasu yankunan Arewa za su yawaita haka. Duk wannan na da nasaba da irin mutane marasa kwarewa da aka dora a kan mukamai. Kenan, dole ne a duba, a tantance, a bawa mutanen da suka dace, ko da kuwa za a yi wa wasu sakayya da kujeru sakamakon wahalar da suka yi, ya zama wajibi a duba gudunmawar da za su iya bayarwa ga ci gaban kasa da kuma jam’iyyar APC.

Ba ka ganin hana wasu mukamai zai iya kawo matsala a cikin APC?

A tsarin siyasa dole ne ka batawa wani, ka birge wani. Mu ne muka kafa APC, me aka bamu? Babu. Ba mu yi rigima da kowa ba, illa iyaka inda muke ganin an kauce hanya mu ce a gyara. Saboda haka shirme ne ma a ce kowa sai an yi masa yadda yake so. Babban abu mai muhimmanci shi ne, a yi abinda ya dace da hankali da tunani, amma shi dan adam ba a iya masa, duk abinda za yi sai ya soke ka ta wani bangaren, saboda haka kiran mu shi ne, a yi adalci, a duba wadanda suka cancanta wajen raba mukaman gwamnati.

Ka yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin APC duk da cewa ka na matsayin jigo a cikinta, shin ba ka ganin yanzu lokaci ne na mara baya ba suka ba?

Dimukradiyya mu ke yi, tsarin da ya bawa kowane dan Najeriya damar fadar albarkacin bakinsa. Babu wanda ya ce sai dan adawa ne zai rika hango maka illa ya fada maka. Gurguwar fahimta ce. Masu iya magana sukan ce mai daki shi ya san inda yake yi masa yoyo. Misali, kwanakin baya sabon Shugaban Majalisar Dattawa Dakta Ahmed Lawan ya nada dan adawa a matsayin mai taimaka masa a fannin harkokin yada labarai, ai matasan APC ne suka yi masa caa a ka, dole ba shiri ya canja. Me kake tsammani da an yi shiru, shi kenan haka za a shigo da baragurbi.

Soyayya da kauna ce ke sanya a fadawa shugaba gaskiya, inda ake ganin ya kauce hanya, a tunatar da shi domin ya dawo kan hanya madaidaciya. Yanzu menene laifin dan Najeriya idan ya ce ci gaba da tsare Sambo Dasuki zalunci ne, ba daidai bane, ya sabawa dokar kasa da ta hankali?

Najeriya kasa da aka gino ta bisa doron kin bin umurni kotu. Da a ce zababbu za su rika mutunta hukunci a mafi yawancin lokuta, ina tabbatar muku da cewa da abubuwa sun dade da canjawa a kasar nan.

Misali, an ce ana zargin Sambo Dasuki da almubazzaranci da kudaden da aka ware domin sayo makamai. Amma abun mamaki, dukkanin binciken da aka yi babu wanda ya nuna inda Sambo Dasuki ya ci adadin wasu kudi ko kuma kudi kada ya bi ta asusunsa. Halin da ake ciki yanzu, babu wani mutum guda da yake tsare game da wannan balahirar sai Sambo Dasuki kadai, duk wani mutum da yake da alaka da kes din yana yawonsa a gari, me ya sa sai shi kadai ne yake tsare, duk da cewa kotu ta bada umarnin a sake domin ya fita kasar waje a duba lafiyarsa.

Idan kana zargin mutum da laifi, ka kai shi kotu, bari za ka yi alkali ya yi aikinsa, hurumi ko ikon hukunci ba a hannunka yake ba kuma; duk abinda shari’a ta zartar da shi za a yi aiki. Saboda haka, ban ga dalili ci gaba da tsare da gwamnatin Tarayya ke yi ba.

Mene ne mafita?

Mafita daya ce, manyan Arewa su sanya baki, domin hakkinsu ne kwatowa namu ‘yanci a duk lokacin da muke ganin ana zaluntarsa. Sambo Dasuki ya bautawa kasar nan iyakacin iyawarsa. Gudunmawar da ya bawa Najeriya bai dace mu zuba ido ana ci gaba da wulakanta shi ba. Mun ga yadda aka yi wa mutane irin su Manjo Hamza Al-Mustapha, bayan an kama shi mafi yawan Arewa juya masa baya suka yi, sai kalilan irinmu muka tsaya kai da fata don tabbatar da ganin an fito da shi, Alhamdulillah yanzu sai dai labari, domin har takarar shugaban kasa ya yi, kuma mutanen da suka juya masa su ne dai suka sake biyo shi gida suna lallabarsa.

Bai kamata mu ci gaba da rayuwa haka ba, a ce sai lokacin da mutum yake cikin jin dadin tukun za ka rabe shi. Halin da ake ciki yanzu, Dasuki yana bukatar daukacin mutanen Arewa su tashi tsaye domin kwato masa ‘yanci. Ba mu ce a yi masa alfarma ko wani abu ba, illa iyaka, a bi umarnin kotu. A ba shi dama ya dawo cikin iyalinsa, in ya so kotu ta ci gaba da binciken ta, kamar yadda ake yi wa sauran.

Akwai matukar mamaki a ce, hatta mutumin da ya sanya hannu wajen fitar da kudi yana nan yana yawonsa cikin gari, ko ina ana ganinsa da daraja. Amma namu dan Arewa, wanda ba shi ya kashe zomon ba, ana ci gaba da tsare ba bisa ka’ida ba.

Saboda haka ina kira ga shugabannin Arewa, wadanda suka san za su iya bada shawara a dauka, su dubi girman Allah, su duba halin da Dasuki yake ciki. Sun sanya baki gwamnatin Tayarra ta bada belinsa, ya koma cikin iyalinsa, ‘yan uwansa da abokan arziki, domin rayuwa idan wata rana kai ne, wata rana kuma ba kai ne ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: