Connect with us

HANTSI

Abubuwan Da Ya Kamata A Kauce Musu Wajen Tarbiyyar Yara

Published

on

Batun tarbiyyantar da yara yana da matukar muhimmanci musamman a wurin iyayen da suke sabon-shiga, ma’ana wadanda suke fara haihuwar ‘ya’ya yanzu-yanzu. Domin taimakon ire-iren wadannan iyayen, mun yi muku nazari game da abubuwan da ya kamata a kauce musu yayin da ake tarbiyyantar da yaran domin samun tarbiyya ingantacciya. A lura da su da kyau sannan a yi aiki da su kamar yadda ya kamata. Ga su:

-Ka daina bai wa yaranka duk wani abun da suka tambaya. Domin za su iya tasowa da tunanin cewa, yana da damar mallakar duk abin da yake da bukata.

-Ka daina dariya a duk lokacin da yaronka ya ambaci Kalmar zagi. Domin za su iya girma da tunanin cewa, raini waniabun nishadi ne.

-Ka daina barin yaranka suna gudanar da dabi’u mara su kyau ba tare da tsawatarwa ba. Domin za su iya tasowa da tunanin cewa, babu wata doka a cikin al’umma.

-Ka daina yarda da duk wata magana da yaranka suka gaya maka. Domin za su iya tashi da tunanin cewa, wasu za su iya daukar nauyin su.

-Ka daina bari yaranka suna bin shirin wasan koikoyo a gidan talabijin. Domin za su iya tashi da tunanin cewa, babu wani bambanci tsakanin babba da yaro.

-Ka daina bai wa yaranka dukkan kudn da suka tambaye ka. Domin za su iya tashi da tunanin cewa, samun kudi yana da sauki, kuma ba za su iya tashi su nema ba.

-Ka daina goyan bayan yaranka lokacin da suka yi wa makwabtanka ba dai-dai ba, ko ma malaminsu ko kuma ‘yan sanda. Domin za su iya tashi da tunanin cewa, duk abin da suka yi dai-dai ne, sannan kuma abin da wasu suka yi ba dai-dai ba ne.

-Ka daina barin yaranka a gida su kadai duk lokacin da za ka je wurin ibada, domin za si iya tashi da tunanin cewa, babu ma Allah gaba daya.

Idan muka bi wadannan abubuwa sau da kafa, to ‘ya’yanmu za su kasance abun kwance a cikin al’umma, kuma za mu yi alfahari a matsayinmu na iyaye.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: