Connect with us

WASANNI

AFCON 2019: Nijeriya Za Ta Kara Da Aljeriya A Wasan Gab Da Karshe

Published

on

Desert Foxes na kasar Aljeriya ta shirya bugawa da Super Eagles na Nijeriya a wasan gab da karshe a gasar cin kofin nahiyar Afrika da ke gudana a kasar Masar. Sun kai wannan matakin ne bayan nasarar da suka samu a ranar Alhamis akan kasar Ivory Coast.

Sun tashi 1-1 ne a wasan su da Ivory Coast din, a yayin da bayan mintoci 120 ne, aka buga bugun daga kai sai mai tsaron gida inda suka yi nasarar doke Ivory Coast din da ci 4-3.

Za dai su kara ne da Nijeriya a filin wasa na Cairo International Stadium a ranar Lahadin nan. Duk wanda ya doke wani, zai isa wasan karshe a gasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: