Connect with us

LABARAI

‘Yan Arewa A Legas Na Murnar Dawowar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zagaye Na Biyu

Published

on

Alhaji Sa’adu Yusuf gulma Mataimakin Shugaban Kungiyar Arewa Community Group dake Jihar ta legas ya yi wannan jawabi lokacin da yake zantawa da wakilin jaridar LEADERSHIP A YAU Juma’a, inda ya nuna farin cikinsa da murna kan dawowar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin hakan zai ba shi damar ci gaban da ayyukan alkhairi ga Kasa.

Bayan haka, a cewarsa, mu ‘yan Arewa mazauna kurmi mun qara samun fahimtar juna da abokan zamanmu a nan Jihar ta legas.

Alhaji Sa’adu Yusuf Gulma ya yi farin ciki da zaben Babajide Sanwo-olu a matsayin Gwamna Jihar ta legas saboda a cewarsa, mutum ne mai karamci da kulawa kan walwalar jama’a, kuma Shugaba ne wanda ya rungumi dukkan al’ummar jihar ta legas ba tare da nuna wani babancin yare ko addini ba, “‘Yan Arewa suna farin ciki,” in ji shi.

Sa’adu Yusuf Gulma ya roqi ‘yan Arewa cewa, “mu hada kanmu don ci gaban wannan Jiha ta legas da Kasa baki daya.”

Shi kuma a nasa bangaren Shugaban kasuwar Alaba Rago Malami ibrahim Ali ya roki ‘yan kasuwa jihar ta Legas da su qara kiyaye dokokin wannan jiha, su zama masu bin doka da oda, kana ya miqa gaisuwar fatan alkhairi ga dukkan Shugabannin ‘Yan Arewa na Jihar Legas da ma Nijeriya baki daya.

Wakazalika, ya nemi a taya Gwamna Baba Jide Sanwo-olu addu’a Allah Ya ba shi ikon ci gaba da hada kan jama’arsa baki daya.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: