Connect with us

FITATTUN MATA

Aloma Mariam Mukhtar: Mace Ta Farko Da Ta Fara Zama Lauya A Arewacin Nijeriya

Published

on

Ko-kon-san?

A yau filin Fitattun Mata na dauke muku ne da tarihin wata fitattacciyar da ta samu yin zarra a duniyar nan, ba kawai a Afirka balle a ce a Nijeriya ba, a’a, a duniyance ma ta samu tagomashin kafa tarihi domin kuwa ita ce mace ta farko a tarihin arewacin Nijeriya da ta fara zama Lauya, kuma babban mace ta farko Alkali a jihar Kano, wacce ta taka matakai daban-daban a rayuwarta tun daga karamin mataki har zuwa ga babban matakin zama Alkali a kotun Koli da kuma Alkali a kotun daukaka kara gami da zama babban Jojin Nijeriya.

Jarumar wato Mai Shari’a Aloma Mariam, wacce take da shekaru 75 a duniya, ta fara aiki a sashin shari’a ne tun shekaru 52 da suka gabata, wacce kuma ta zama daga cikin wadanda tauraronsu ya haska sosai a hidimar shari’a a wannan kasar.

Wace Ce Aloma Mariam Mukhtar?

Aloma Mariam Mukhtar dai an haifeta ne a ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar 1944 wacce ta fito daga jihar Kano da ke arewacin Nijeriya. Ta halarci makarantar Firamaren Saint. George’s da ke birnin Zariya, ta kuma halarci St. Bartholomew’s School da ke Wusasa a Zariya, ta kuma garzawa zuwa makarantar ‘yan mata ta Rossholme, East Brent, Somerset da ke kasar Ingila ta kuma je Berkshire da ke Ingila, sannan ta halarci kwalejin koyar da ilimin shari’a Gibson and Weldon da ke kasar Ingila wacce hakan ya kai ta ga samun damar a kirata da suna mai daraja ta ‘English Bar’ wato cikakken Lauya a watan Nuwamban shekarar 1966 a shekarar 1967 kuma ta zama Lauya a Nijeriya mai cikakken ikon gudanar da aiki a matsayin Lauya.

Aiyukanta a fannin Shari’a:

Madam Mariam Mukhtar ta fara aiki ne a shekarar 1967 a matsayin Lauyar jihar Kano, ta yi aiki a karkashin ma’aikatar shari’a a arewacin Nijeriya wacce ta takara matakai daban-daban a wannan wurin aikin da ta yi.

A shekarar 1971 ne ta gudanar da aiki a sashin shari’a a ofishin Draftman, ta yi aiki a ofishin Interim Common Serbices Agency, ta zama Alkali a kotun Majistiri mai madaraja ta I.

Ta zama babban magatakardar kotu a karkashin gwamnatin jihar Kano a shekarar 1983, ta zama Alkalin babban kotu a jihar Kano a tsakanin shekarar 1977 zuwa 1987, har-ila-yau likkafarta na ci gaba da cillawa inda ta zama Alkali a kotun daukaka kara ta Nijeriya da ke Ibadan daga shekarar 1987 zuwa 1993.

Gogewar nata a bangaren ya shari’a ya kuma kai ta ga zama Alkali a kotun Koli ta Nijeriya daga shekarar 2005 zuwar zuwa shekara 2012 tana gudanar da aiki a matsayin Alkali a kotun koli ta Nijeriya. A shekarar 2011 zuwa 2012 ta zama mai shari’a a kotun Koli ta kasar Gambia.

Ta zama babban mai shari’a a Nijeriya (Chief Justice of Nigeria) daga watan Yuli na shekarar 2012 zuwa Nuwamban shekarar 2014.

Tarihin fannin shari’a a Nijeriya ba zai taba kammaluwa ba sai an jero irin su Mariam Muktar domin kuwa ta kasance mace ta farko da ta fara zama a mukamai daban-daban wanda hakan ya sanya sunanta ya zama wani alamin dubawa ga maza da mata a Nijeriya musamman wadanda suke da alaka da sashin Shari’a.

Ita ce mace ta farko dukkanin fadin arewacin Nijeriya da ta fara zama Lauya, ita ce mace ta farko da ta fara zama Alkalin babban kotu a jihar Kano, ita ce mace ta farko da ta zama Alkali a kotun daukaka kara, mace ta farko da ta fara zama Alkali a kotun Koli a Nijeriya, mace ta farko da ta hau kujerar babban Jojin Nijeriya.

A ranar 16 ga watan Yuli shekarar 2012 ne shugaban Nijeriya a wancan lokacin Goodluck Jonathan ya rantsar da Mukhtar a matsayin babban Jojin Nijeriya hadi da sanar da lambar yabo ta kasa mai matukar daraja ta (GCON).

Lambobin Yabon Da Ta Amsa A Rayuwa:

Madam ta samu lambobin yabo da jinjina masu tarin yawa a ciki da wajen kasar nan masu daraja a bisa zamanta fitattacciya jaruma a wannan karnin, kadan daga cikinsu sun hada da lambar yabo ta Commander of the Order of Niger in 2006, a shekarar 1993 ta amshi lambar yabo na zinariya mai daraja a bisa kokarinta kan daukaka ci gaban jihar Kano ta fuskacin shari’a, sannan ta kuma samu lambar yabo ta Nigerian Hall of Fame a shekarar 2005 da wasu tulin lambobin yabo da jinjina musamman ganin yadda ta zurfafa ta fadada iliminta da kokarinta wacce har ta yi zarra a duniyance ma ba kawai a Nijeriya ko Afrika ba.

Madam Mariam tana daga cikin matan da suka fara aikin Lauya a duniyance, ‘First Women Lawyers Around the World’.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: