Connect with us

LABARAI

An Aike Da Sunan Mukaddashin Alkalin-Alkalai Na Kasa Domin Tabbatar Da Shi

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunan mukaddashin alkalin alkalai Ibrahim Tanko Muhammad ga Majalisar dattijai domin tabbatar da shi a matsayin babban alkalin Nijeriya.

Shugaban kasar ya nemi wannan bukatar ce a wata wasika da ya aikawa da Majalisar a jiya Alhamis wadda kuma aka karanta ta a gabanta.

An nada  Muhammad a matsayin mukaddashin alkalin alkalai ne a cikin watan Janairun wannan shekarar, bayan da wata takaddama ta kaure wadda ta yi sanadiyyar dakatar da tsohon Babban alkalin na kasa Walter Onnoghen, bisa zargin kin bayyana gaskiyar kaddarorinsa.

A ranar Larabar da ta gabata ne Hukumar kula da alkalai ta kasa ta  mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari sunan mai shari’a Tanko domin amincewa a matsayin Babban alkalin Nijeriya.

Bayan  amincewar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kan wannan bukata, a halin yanzu ya tura sunan gaban Majalisar dattawa domin ta tabbatar da shi a matsayin babban alkalin Nijeriya
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: