Connect with us

LABARAI

An Sake Yunkurin Juyin Mulki A Sudan

Published

on

Gwamnatin soji ta riko a Sudan ta sanar da dakile yunkurin juyin mulki a ranar Alhamis tare da cafke jami’an tsaro 16 da ake zargi da hannu a lamarin. Jagoran kwamitin gwamnatin hadaka da sojoji ke jagoranta Janaral Jamal Omar Ibrahim ne ya sanar da hakan a wani jawabi da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin din kasar.

Ya kara da cewa biyar daga cikin wadanda aka cafke sojojin da suka yi ritaya ne da wadanda ke bakin aiki. An kuma sake kama wasu mutum hudu na daban da su ma ake zargin suna da hannu a yunkurin.

Sai dai bai yi karin haske kan rana da lokacin da lamarin ya faru ba, Janaral Jamal ya ce yunkurin wani salo ne na kawo cikas kan yarjejeniyar da sojoji da shugabannin farar hula suka cimma na kafa gwamnatin hadaka.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da masu bai wa sojin shawara da shugabannin masu zanga-zanga ke ganawa a birnin Khartoum. Domin ci gaba da samar wa ‘yan kasar matsaya kamar yadda masu shiga tsakanina kungiyar Tarayyar Afirka da kasar Habasha suka fara a makon da ya gabata.

Dangantaka tsakanin sojoji da farar hula ta yi tsami tun bayan hambarar da gwamnatin Tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashar daga mukaminsa wanda ya shafe shekara 30 a kai.

Da fari sojojin ne suke taimakawa masu bore har suka cimma nasara, to amma matakin jan ragamar kasar da sojin suka yi ya kara fusata ‘yan Sudan da suke kallon ba ta sauya zani ba saboda a ganinsu sojojin suna nan a matsayin yaran tsohon shugaban.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: