Connect with us

WASANNI

Arsenal Na Kan Gaba Wajen Neman Ceballos

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ce akan gaba wajen neman dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Dani Ceballos, bayan da Real Madrid din ta bayyana cewa dan wasan nata na sayarwa ne.

Duk da cewa dan wasan baya son barin Real Madrid amma Real Madrid ta bayyana cewa ba ta bukatarsa a wannan lokaci kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka saka a kasuwa domin sayarwa a kokarin da sukeyi na samun kudi domin sayan Pogba.

A kwanakin baya aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ce akan gaba wajen neman dan wasa wanda a watan daya gabata ya jagoranci tawagar kasar Sipaniya ta lashe gasar cin kofin nahiyar turai na ‘yan kasa da shekara 21.

Sai dai wasu jaridu daga kasar Sipaniya sun tabbatar da cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ce akan gaba wajen zawarcin dan wasan kuma tuni Magana tayi nisa tsakanin kungiyoyin biyu yayinda tuni dan wasan ya amince da komawa Arsenal din.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, yana ganin Dani Ceballos ne kawai zai iya maye masa gurbin Aaron Ramsey, wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Jubentus a kyauta a karshen kakar data gabata.

Har ila yau Arsenal tana cigaba da zawarcin ‘yan wasan Real Madrid guda biyu, Lucas Baskues da kuma Mariano Diaz wadanda duka Real Madrid din ta tabbatar musu da cewa basa cikin tsarinta na kakar wasa mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: