Connect with us

MAHANGA

Batun Yaki Da Fasa-kwaurin Shinkafa

Published

on

Manoman shinkafar gida da sauran masu sarrafa da kuma cinikin ta sun yanke shawarar tsayar da farashin bai daya don tunkarar yaki da fasa-kwaurin shinkafar waje a duk fadin kasar nan. Fatansu shi ne, idan wannan doka ta fara aiki ka’in da na’in, akwai yiwuwar shinkafar gidan ta zo ta yi kan-kan-kan da ta wajen a kasuwa ko ma ta fi ta sauran kudi. Dalili kuwa, Shekaru biyu da suka wuce da aka haramta shigo da shinkafar wajen ta barauniyar hanya, haka aka ci gaba da haramta shigo da itan.

Wannan ne ma ya sanya Kungiyar Manoman Shinkafa na Nijeriya (RFAN) tare da Kungiyar Masu Sarrafa ta  da Cinikinta na Nijeriya (RPAN), kwanan nan suka bayyana aniyarsu ta karyar da farashin shinkafar gidan mai dauke da nauyin kg 50 daga Naira 15,000 zuwa Naira 10,000, kafin karshen wannan shekarar.

Manoman dai sun sha alwashin noma shinkafar mai tarin yawa wanda a cewarsu, zai taimaka matuka gaya wajen rage farashin samfarera daga Naira 11,000 zuwa Naira 8,000 a halin yanzu. Kazalika suka kara da cewa, farashin gyararriyar shinkafa kuma ya jima yana faduwa tsawon shekara da shekaru sakamakon hana fasakwauri da aka yi, wanda hakan kuma zai sa farashin ita ma shinkafar gidan ya sakko. Saboda haka, da zarar farashin samfarera ya yi kasa, wajibi ne shi ma na gyararriyar shinkafar ya sauka.

A wannan gaba, wannan Gidan Jarida ya yaba da wannan mataki da wadannan Kungiyoyi na Manoman shinkafa da kuma masu sarrafa ta suka cimma matsaya a kai. Dalili kuwa shi ne, mun yarda da cewa idan har masu ruwa da tsaki za su yi wa shinkafar gida farashi wanda zai iya yin kan-kan-kan da na wanda ake shigo da ita ta barauniyar hanya, ko shakka babu za a iya ganin canji.   

Amma mu a namu ganin, idan har ana so wannan doka ta tafi yadda ya kamata, to fa wajibi ne sai Hukumar hana fasakwauri ta kasa (Custom) ta sake mikewa tsaye wajen hana shigo da wannan shinkafa da waje. Don kuwa, Kamfanonin Nijeriya musamman na shinkafa na matukar fuskantar barazanar karyewa, sakamakon mamayar da shinkafar waje ta yi a kasuwannin wannan kasa.   

Kusan dukkanin kasuwannin kasar nan idan ka zaga, babu abin da za ka gani sai shinkafar waje a Sito-sito makire da shinkafar waje wadda ingancinta da kuma tabbacin lafiyarta abu ne da y a zama wajibi a binka kafin a kai ga cinta ko sayar da ita.

Kamar yadda Hukumar Kwastan ta bayyana, Shinkafa ita ce abu mafi yawa da aka fi yin fasakwaurinta a wannan kasa, wadda kuma ke daukar kusan kaso 70 cikin 100 na shinkafar da ake sayar da ita a cikin fadin kasuwanmu, yake kwashe kaso mai tsoka na kudaden da muke fita da su kasashen waje.   

Har ila yau, ‘Yan kasuwa sun zuba kudadensu da dama a harkokin shinkafa a Nijeriya, sai dai kash, abin da ya hana Kamfanonin nasu ci gaba tare da habaka shi ne, matsalar fasakwauri. Kamar yadda Manoman shinkafar suka bayyana, a cikin watanni uku kadal, an shigo da shinkafa ta barauniyar hanya (fasakwauri) kimanin buhu Milyan 20 Nijeriya.

Kazalika, binciken da Leadership A Yau ta yi ita ma ya nuna cewa, fasakwaurin shinkafar da ake yi ta hanyar shigo da wannan kasa, ta hanyar Kasar Niger  ce da Benin. Misali, daga Jihar Ogun da kuma Legas, za ka samu cewa ana sayar da shinkafar da ake shigo da ita daga Naira 5,000 zuwa Naira 6,000, saboda masu shigo wa da ita daga Kasar Benin ko Kwatano.

A halin da ake ciki yanzu, Nijeriya na tafka asarar kudaden shiga kwarai da gaske, sannan masu Kamfanin shinkafa a bangare guda na tafka su ma irin tasu asarar da yake sanadiyyar rufe Kamfanin nasu sakamakon rashin samun karbuwa a kasuwanni.

Babban abin damuwar yanzu shi ne, yadda shinkafar da ake shigowa da ita yanzu ke dauke da mataccen sinadaran

Magunguna, sannan ake canza wa wadanda tuni suka riga suka tashi daga aiki, ma’ana lalatattu wadanda wa’adin da aka diba musu suka kare buhunhuna, wanda suka haura shekaru ashirin a ajiye bakin Teku, ana kawo ana sayar wa mutane.The most

A nan, muna kira ga Gwamnati da ta hana shigo da shinkafa daga kasashen waje kwata-kwata, idan ba haka ba kuwa, Kamfaninnikanmu na cikin gida za su ci gaba durkushewa. Sannan ta sani cewa, sakamakon bari da aka yi ana shigo da wannan shinkafa, asarar kudaden shiga da wannan kasa ke yi ba karami ba ne, ban da kuma asarar da ake tafkawa ta bangaren masu neman aikin yi sakamakon Kamfaninnikan da a koda yaushe a rufewa saboda rashin samun kasuwa a kasuwanninmu.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: