Connect with us

RAHOTANNI

Hajjin Bana: Ganduje Ya Bukaci Mahajjatan Kano Su Kasance Masu Bin Doka A Saudiyya

Published

on

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci Mahajjatan Jihar

Kano su kasance masu kiyaye doka da oda a lokacin gudanar da ibadar ayyukan Hajji na bana a Kasa Mai tsaki. Gwamnan ya yi wannan kira ne, a yayin gudanar da nuna samfurin ayyukan Hajji a aikace da aka aiwatar ga maniyyatan Jihar Kano a sansanin Alhazai da ke Jihar.

Mataimakinsa Gwamnan Jihar, Dakta Nasiru Yusif Gawuna ne ya wakilci Mai girma Gwamnan a wajen taron, ya kuma ja hankalin Maniyyatan da su kasance nagartattu, masu tafiyar da komai nasu cikin tsari a matsayin su na wadanda za su je ibada wannan kasa mai tsarki, su kuma tabbata da cewa, ko sun sani ko ba su sani ba, su wakilan  Jihar Kano ne kuma wakilan Nijeriya baki daya. sannan, ana bukatar Maniyyatan su kaucewa duk wasu munanan ayyuka da ka iya

zubar da kimarsu da kuma ta Jihar Kano a yayin wannan ibada da za su je.

“Alhazai daga Jihar Kano a koda yaushe, an san su da kyawawan dabi’u tun daga lokacin tashinsu daga nan Kano har zuwa Kasar Mai tsarki, haka kuma ake fatan za su ci gaba har zuwa lokacin dawowarsu gida Nijeriya.

Wannan ce tasa a shekarar da ta gabata 2018, Kasar Saudiyya ta bayar da lambar yabo ga Hukumar Alhazan Jihar Kano, kansacewar su ne suka fi kowacce Jiha gudanar da kyawawan halaye a lokacin aikin Hajjin.”

“Ko jiya ma, sai da Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa, Barister  Abdullahi Mukhtar  ya zo Kano domin gudanar da ziyarar aiki, inda ya bayyana Gwamnatin Jihar Kanon a mai ci a halin yanzu  da cewa, ita ce Jihar da ta aiwatar da mafi ingancin  tsarin harkokin jin dadin Alhazan a fadin kasar nan baki daya.” In ji shi.

Kamar ko da yaushe, Ganduje na bayyana cewa, an samar da karin kwararrun Ma’aikatan lafiya, tare da samar da ingataccen tsaro wanda zai tafi tare da Alhazan domin ci gaba da taimaka masu a Kasar ta Saudiyya. Haka kuma, ya sake bayyana cewa, Gwamnatin Kano ta rattaba hannu  da wasu kwararrun Malamai wadanda aka dora wa nauyin wayar da kan Mahajjatan a kan harkokin da suka shafi ayyukan Hajjin na bana.

Da yake taya  murna  ga Maniyyatan bisa zabar su da Allah Ya yi domin gudanar da aikin Hajin wannan shekara, haka kuma ya sanar da cewa Jihar Kano za ta bayar da tallafin Riyals 50 na Saudiyya ga kowanne maniyyaci daga Jihar Kano.

Tun da farko, babban Sakataren Hukumar jin dadin Alhazan Jihar  Kano, Alhaji Muhammad Abba Danbatta, ya fadi cewa bayan gudanar da aikin Hajjin shekarar da ta gabata ta 2018, Hukumar ta  gudanar da taruka daban-daban  domin yin nazarin nasarorin  da aka samu. Wannan ce ta baiwa Hukumar damar fito da sabbin  tsare-tsare wadanda za su kara inganta hanyoyin samun nasarar aikin Hajji a nan gaba. Sannan ya sake bayyana cewa,  Hukumar  ta samar da wasu cibiyoyi  guda 16 domin wayar da kan Mahajjata, daga bisani kuma aka kara fadada cibiyoyin zuwa guda 32 a fadin wannan Jiha baki daya.

Hakazalika, Abba ya gode wa gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bisa ci gaba da goyon bayan da take baiwa wannan Hukuma, wanda shi ne kashin bayan dukkan nasarorin da muka cimma. Kamar yadda Sakataren yada Labarai na Mataimakin Gwamnan Kano, Hassan Musa Fagge ya shaida wa Jaridar Leadership A Yau Juma’a.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: