Connect with us

MAGUNGUNA A MUSULUNCI

Hanyoyin Rigakafin Ciwon Farfadiya

Published

on

Kamar yadda muka yi bayanin Farfadiya a makon da ya gabata, har ma muka ce ta kasu kashi shida, kuma muka yi bayanin ta farko wacce ita ce take fitar da kumfa daga baki, kuma ita ce take faruwa daga rashin lafiya da take haifarwa a cikin jiki har muka zo kan hanyar riga-kafinta. Mun ji hanyoyi guda hudu da ake riga-kafin wannan cutar ta Farfadiya, don kar ta kama mutum. Saboda haka ba sai mun maimaita ba.

To hanya ta gaba ita ce, motsa jiki, saboda rashin motsa jiki yana kashe ko wane jiki, ko wani bangare na jikin, saboda haka wannan bangare sai ya daina aiki yadda ya kamata, to yayin da mutum ba ya motsa jikinsa, to daga nan ne yake fara kamuwa da cuta daga cikin bangarorin jikinsa shi ne cikinsa, zai samu rikicewar dabi’unsa, don haka sai Injinan narka abinci na cikinsa su samu rauni wurin narka abinci da markada shi, saboda haka mutum yana iya samun ciwon hauhawar kitse, ta mugunyar ruwan da mukai maganar cewar yana iya toshe hanyoyin wasu jijiyoyin kai sako kwakwalwa, kuma jinin jikin mutum ma yana iya gurbacewa.

Saboda haka a irin wannan yanayin cututtuka za su faruwa, kuma daga cikinsu akwai wannan cutar ta Farfadiya. Kuma yin Istifragi yana taimakawa matuka wajen hana kamuwa da annan cutar da yardar Allah Ta’alah. Istifragi shi ne ato wanke jiki da fitar da dauda da cushewar daga jiki da wanke jini da tsaftace shi da yake ko ina daga cikin jijiyoyin jiki. Ya ‘yan uwa kullum muna kara gaya maku cewa Wallahi duk matsalolin da muke ciki a halin yanzu mafi yawa saba wa Allah da Manzon Allah ne.

Saboda idan za mu bi abinda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya zo mana da shi za mu zauna lafiya,  kuma idan ma wata matsala ce ko wani ciwo ya same mu, to mu fara amfani da maganin da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya zo da shi, iya yin mu ba sai mun fara amfani da wasu magumguna ta wasu hanyoyi mun ga ba mu samu lafiya ba, sannan mu ce za mu dawo mu nemi na musulunci ba, Saboda yin hakan yak an sawa in aka doso wurinmu sai an sha wahala kafin a dace, saboda dukkanmu musulmai ne, kuma bai kamata ace mutum ga abu a gidansu sai ya fara amfani da na gidan wasu ba, in bai masa kuma ya ce bari ya koma na gidansu.

Ya ‘yan uwa abinda ya sa nake wannan maganar, Manzonmu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi , da yake son duniya gaba daya da rahama, Allah Ta’alah ya fada game da shi cewa “ Lakad jaa’akum Rasuulun min amfusikum azizun alaihi maa anittun harisun alaikum bil mu’u minina ra’uufurrahim”

Wato kakika manzo ya zo maku daga cikinku, kuma duk abinda ya same na matsi ko ciwo shi ma yana damunsa, saboda shi maia matukar so ya yi maku duk wani alheri ne, kuma ga Muminai mai matukartausayi ne.” ya gaya mana yadda za mu rika wanke daudar jikinmu wanda zai zamar mana riga-kafin wannan cuta ta Farfadiya da ma wasu cututtuka masu wuyar magani. Kamar yadda ya zo a cikin Ibnu Maja’a da Tirmizi da kusan duka littattafan likitanci manya daga Asma’a bintu Umais Allah ya kara mata yarda ta ce, “ Sa’alani Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, Bi maazaa tastamnshin?” wato manzon Allah tira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tambaye ni cewa, da me nake wanke cututtuka ko kuma na hana su faruwa?”

Sai n ace masa (Bi shubrun)  kamar yadda muka sani shi dai Shibrun wani itace ne mai kama da tazargade, sai ya ce “Harrun jarrun”  wato “Wannan bishiya tana da zafi, kuma tana da kwaranyarwa da yawa, saboda haka sai ya ce min na yi amfani da (Sana) har kuma ya kara min da cewa “ In kaana fi shai’in shifa’un minal mauti, lakad kaana fissana.”  Da ace akwai wani da zai yi maganin mutuwa to da na farkonsu (Sana)ce, saboda tsananin amfaninta ga jikin dan Adam.

Kamar ya kara zuwa a wata riwayar wadda har Imamu Bukhari ma ya ruwaice ta, cewa Mnazon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi y ace “ Assana wassunut fihimaa dawa’un min kulli da’in.”

wato “ Ita wannan Sana din da muke magana a kanta, da kuma Sutu, suna magance ko wace irin cuta.”  Bayin Allah mu lura, shi Manzon Allah mai tsira da amincin Allah zai gaya mana magani ne a dunkule, kada mutum ya ga ya yi magani bai yi ba, ya ce maganin ba ya yi, a a sam bah aka bane, wata kila bas hi ka samu ba, ko kuma ba mai kyau ka samu, ko kuma ba hada shi yadda ake hada shi yadda zai yi maka maganin irin cutar ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: