Connect with us

BABBAN BANGO

Harshen Sinanci: Gadar Huldar Sin Da Afrika

Published

on

Akwai wani karin magana na Larabaci dake bayyana cewa: “Za a kaucewa wani yaki idan an iya wani harshe na daban”. Saboda ganin haka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a wani jawabi da ya yi a asusun Koerber da ba na neman cin riba ba a birnin Berlin, fadar mulkin kasar Jamus cewa, kara fahimtar juna zai taka muhimmiyar rawa wajen zurfafa, da habaka cudanya da hadin kan Sin da Afrika.

Harshe, tushe ne na fahimtar juna, kuma ya kasance tubali mai muhimmanci a huldar kasa da kasa. Kana kuma daya ne daga cikin wasu muhimman mataki na bunkasa wayewar kan Bil Adama, kana yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya.

Sinanci wato Mandarin a Turance, na zama muhimman mataki ga raa huldar Sin da Afrika, wanda ba za a iya maye gurbinsa ba ko kadan, wanda ya ba da gudunmawarsa sosai a cikin wasu manyan ayyuka, ciki hadda hadin gwiwar Sin da Afrika don tabbatar da ajandar shekarar 2063 na Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ajandar samun ci gaba mai dorewa na shekarar 2030 na majalisar dinkin duniya ta MDD, kana da shirin hangen nesa kan bunkasuwa na shekarar 2030 kuma da shirin samar da kayayyaki na shekarar 2025 na kasar Sin da dai sauransu.

Ya zuwa yanzu, yawan mutane da suke yin amfnai da Sinanci ya kai bilyan 1.2, kashi 70 cikin dari ne daga cikin wadannan mutane Sinawa ne. Wanda ya zama harshe ne da mutane mafiya yawa a duniya ke yin amfani da shi, Spanish, Turanci da Larabci kuma na biye masa baya. Yawan mutane da suke yin amfani da su ya kai miliyan 437 da milyan 372 da kuma milyan 295.

Amma, yawan ‘yan Afrika da suka iya Sinanci ba su da yawa, idan an kwatanta da Faransanci, Turanci, harshen Portugal da Larabci, saboda ba kamar kasashen Faransa, Birtaniya da Portugal ba, Sin ba ta taba gudanar da mulkin mallaka a Afrika ba.

Tun bayan aukuwar yakin wiwi karo na farko a shekaru 40 na karni 19 a kasar Sin, Sinawa na nacewa ga wani karin magana na gargajiya, wato “Wanda ba ya so a kawo masa illa, to kada ya kawo illa ga saura.”

Yaduwar Sinanci da kwalejojin koyar da Sinanci ya biya bukatun mu’amalar jama’a da kasuwanni, ba shi da alaka da tsarin mulkin mallaka ba. Kuma ya kasance wani mataki mai amfani ne ga kasashen da shawarar “Ziri daya da hanya daya ” ke shafa.

Kungiyar yada Sinanci ta kasa da kasa ta ba da bayanin cewa, yanzu an kafa kwalejojin Confucius fiye da 480 a jihohi 6 na duniya. A ran 19 ga watan Disamba na shekarar 2005, an kafa kwaleji na farko a nahiyar Afrika a birnin Nairobi, fadar mulkin Kenya. Har wa yau, kwalejin na yaduwa zuwa cibiyoyi 54 a Afrika, wato kasashen Afrika 33 na da shi. Ban da wannan kuma, akwai ajin koyar da Sinanci 27 a Afrika, idan a yawansu a Afrika ta kudu da Habasha ya fi yawa, ko wace tana da aji 5. Habaka wadannan kwalejojin Confucius da ajin koyar da Sinanci da kwalejojin yada al’adun Sin, mataki ne da Sin take dauka a Afrika don kara tuntubar juna, wanda aka tabbatar da shi a taron shekara-shekara karo na 4 na dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC da aka yi a birnin Johannesburg, fadar mulkin Afrika ta kudu, a shekarar 2015, daftarin da dandalin ya zartas a gun taro na nuna cewa, Sin za ta goyi bayan kafa karin kwalejojin da ajin a Afrika.

Sin na da al’adu mai kayatarwa, dake da daddaden tarihi na tsawon shekaru fiye da 5000. Hukumomin yada Sinanci da Sin ta kafa a Afrika sun kai kimanin 50.

Sinanci ya zama darasin zabe ne a Afrika ta kudu a shekarar 2014, ya zuwa shekarar 2017, yawan makarantu da suke da darasin Sinanci ya kai 53. A Zambiya kuma, Sinanci na samun karbuwa sosai, har jaridar Times of Zambia ta rubuta wani labari da Sinanci a shekarar 2018.

Ban da wannan kuma, a Uganda, an shigar da Sinanci a cikin darusa, kana a Kenya kuma, tana shirya koyar da ilmi da Sinanci daga shekarar 2020, daga aji na matki na 4 na firamare.

Duk matakan da suka dauka na nuna karbuwa ga Sinanci, na kara bunkasa huldar Afrika da kasar Sin.

A Nigeriya kuma, a ran 7 ga watan Maris na shekarar 2008, an kafa kwalejin Confucius ta farko a Nigeria a jami’ar Nnamdi Azikewe, dake kudu maso gabashin kasar, shugaban hukumar ba da ilmi da shugaban hukumar yada labarai na jihar Anambra sun halarci bikin. Tsohon karamin jakadan Sin mai kula da harkokin al’adu dake Nigeria Jiang Weiming ya ce, harshe wata gada ce ta tuntubar al’adu, wannan kwaleji ta farko za ta zama ta bude wata taga ga Nijeriya, wadda za ta taimakawa jama’ar kasar wajen kara fahimtar kasar Sin. Daga baya kuwa, a ran 16 ga watan Octomba na shekarar 2009, an kafa kwaleji na biyu a jami’ar Lagos, tsohon shugaban jama’ar ya bayyana a gun bikin budewa cewa, kwalejin dai na da ma’ana sosai wajen kara hadin kan Sin da Nijeriya a fannin ala’du, jama’ar na goyon baya kwarai da gaske kan gudanar da wannan kwaleji yadda ya kamata.

Ba da dadewa ba da na isa Nijeriya a shekarar 2016, na kai ziyara a kwalejin Confucius dake Lagos, don ganin yadda ake gudanar da aikin koyar da Sinanci da yada al’adun kasar Sin a Nijeriya. Lokacin da na isa kwalejin, na yi mamaki sosai, saboda suna da na’urori na zamani da dalibai da dama. An ce, jami’ar Lagos da jami’ar mai koyar da ilmin kimiyya wato BIT a Turance, sun yi hadin kai don kafa wannan kwaleji a ran 9 watan Octomba na shekarar 2008, kuma an fara yin amfani da ita a ran 25 ga watan Mayu na shekarar 2009, yanzu kwaleji na da ofisoshi 6 da dakin ajiye litattafai 1, da daki mai na’urorin zamani 1, da dakin koyon sautin Sinanci1, cibiyar nune-nunen al’adun Sinanwa 1 wanda fadinsa ya kai murabba’in mita 293. Ban da wannan kuma, suna da rukunin malamai masu kwarewa sosai dake kunshe da malaman da jami’ar BIT ta tura wurin su 2 ,da masu sa kai 10, dukansu na da digiri mai kyau a fannin koyar da Sinanci da fasahar koyarwa. Saboda ganin fitattun ayyukan da kwalejin ke yi ta fuskar koyar da Sinanci da yada al’adun Sin, gwamnatin jihar Lagos ta shigar da kwas din Sinanci cikin makarantar midil ta Lagos, kuma a karo na farko an shigar da kwas din Sinanci a cikin tsarin samar ilmi na Nijeriya. Dadin dadawa, kwaleji kuma ta kafa cibiyar jarabawa ta HSK, don tantance yadda daliban Nijeriya suke koyon Sinanci, yawan dalibai da suka shiga wannan jarabawa kafin shekarar 2013 sun kai fiye da 300. Kwalejin kuma, na yin hadin kai da jami’ar Lagos don kafa gidan rediyon watsa labarai na Sinanci, wanda ke gabatar da shirye-shirye na mintoci 20 sau biyu ko wace rana. Haka zalika kuma, kwalejin na mai da hankali sosai kan musanyar al’adu a wurin, yana gabatar da gasar gadar Sinanci karo na farko a Nijeriya, da kuma watan al’adun kasar Sin karo na farko da dai sauran ayyuka da dama, matakan da ya jawo hankali kafofin yada labarai da kungiyoyin al’adu na Nijeriya. Wani dalibi mai suna Usman ya gaya mini cewa, dangoginsa da dama suna ciniki a kasar Sin, shi ma yana fatan koyon Sinanci don wata rana ya iya kai ziyara a birnin Guangzhou kuma ya tafitar da ciniki a wurin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: