Connect with us

ILIMI

Hattara

Published

on

Shin ko ka san ya za koyi yadda ka ka rangado tambayoyi masu cike da ma’ana a aji?

Daya daga cikin dabi’ar da aka San mafi yawan dalibai da ita, ita ce, ba za ka raba su da yawan tambaya mai kama da ‘ba-komaz-baya’, abin da ya yi kama da: ba su fahimci inda darasin ya fuskanta ba. Kuma a lokuta da yawa su yi kafe kan abin da sauran daliban suka fahimta kenan a tambayar. Abokina, shin a lokaci bayan lokaci, kana fuskantar matsalar yin tambaya a aji- alhalin kuma ka na da abin tambaya?

Ga wasu ‘yan matakan da za su taimaka maka wajen kwarewa a fagen tambaya mai ma’ana.

Da farko ka cire tsoro da shakku daga zuciyar ka:

Mataki a nan kuma shi ne, ka yi tunani kan wane dalili ne ya sa kake yawan samun shakku ko karaya, sai ka kaurace masu. Ka yi wa kanka kaimi tare da samun yakinin cewa rayuwar ka tana cikin garari matukar za ta hana ka tambayar abin da ba ka sani ba, ko tsoro, shakku tare da rashin yarda da kan ka, a zaman ka na makaranta.

Ka zama natsattse:

Kana da tambaya a zuciyar ka, ko neman karin bayani dangane da wani abu da ya shige ma duhu, sabida haka a natse za ka daga hannunka da tambayar malamin ka, don ya taimake ka wajen warware maka wasu damuwar ka.

Ka koyi yanda za ka iya yin bayani da kanka:

A duk lokacin da malamin ku ya ba ka damar yin tambaya ko neman karin bayani, ka yi iya tunani da kokarin yanda za ka yi masa gamsasshen bayani kan damuwar ka. Misali, sai ka ce: Yallabai, har yanzu ban fahimci bayanin ka ba, idan babu damuwa a kara fayyace min lamarin dalla-dalla.

Ka bude bakinka, ka yi magana  kowa ya ji:

Yana da gayar muhimmanci, ka tabbatar kan cewa ka yi bayani kai tsaye kuma a cikin tsanaki har malamin ya fahimci abin da kake fada da kyau. Yayin da wani abin mamaki shi ne, za ka  ga dalibi yana kokarin neman karin bayani amma kuma malami ba ya jin abin da kake kokarin ka gaya masa, wannan ya na jawo malami ya kaucewa tambayar ka.

Ka tabbatar ka yi tambayar ka a bangaren da ka gane abin da ya kunsa:

Saboda haka, kafin ka yi tambaya to ka tabbatar da cewa ka yi wa abin da za ka yi tambayar a kan sa sauraren ta-natsu, a lokacin da yake koyar da ku. Sannan kuma, bayan ka kammala rangado tambayar, ya na da kyau ka nuna wa malamin kan cewa ka fahimci yankin darasin sa, hakan zai nuna masa kan cewa kai ma fa kwallo ne- kana fahimtar karatu kenan.

Sa’ilin nan kuma, sai ka yanko bangaren da kake son karin bayani daga darasin:

Wanda bayan kammala tabbatar masa bagiren da ka fahimta a wannan darasi nashi, saboda haka a cikin tsanaki sai ka bukaci ya taimaka maka da yin bayanin inda ba ka gane ba sosai.

Wannan shi zai bai wa malami gano hakikanin inda ka gane kuma a ina ne kake bukatar karin haske  tare da taimako, tare da yanda ka tunkare shi da tambayar ka da sanin cewa lalle yanzu ka kama hanyar da yake nuna maka.

Ka rinka tsayar da tunanin ka wuri guda:

A matsayin ka na dalibi, kar kana  harbin iska dangane da bagiren da aka doraka, ka yi tambaya kai tsaye, kuma ka kaucewa yawaita tambayar shiga sharo ba shanu- tambayoyi maras amfani. Saboda inna-rididin bayanai suna jawo ba ka amsar da ta yi hannun riga da matsalar ka, kuma sakamakon kanka zai koma ba a kan malamin ba.

Ka nisanci amfani da kalmomi maras ma’ana:

Kalmomi irin su “um”, “ermm”, da makamantan su, kalmomi ne maras cikakkiyar ma’ana. Kuma a duk lokacin da dalibi ke kokarin ya ce wani abu ko tambaya, to ya yi iya kokarin nisantar irin wadannan kalmomin.

A karshe yanzu kam za ka iya jefa tambayar ka:

Abokina, a daidai wannan gabar, maimakon ci gaba da zama da dimbin matsalolin da ke addabar ka, yanzu kam za ka iya gwada yin tambaya. Sannan kar ka manta, zakakuran hazikan dalibai ne kadai kan jefa tambayoyi dangane da lamurran da ke yi musu kaikayi a kirji ko idan wata bukatar da ta shige musu duhu ta taso. Saboda haka, kar ka ji tsoron yin tambaya mai ma’ana, amma kuma ba kowane malami ne zai jure tambayar rashin kan gado ba.

Bugu da kari kuma, ina tsammanin kawowa yanzu ka gano bakin zaren, ko!
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: