Connect with us

RAHOTANNI

Kasashen Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Ziyarta Ba Tare Da Biza Ba

Published

on

A kowane lokaci Yin tafiya ga ‘yan Nijeriya abu ne da yake da bukatar yin shiri sosai. Tare da cewa, fasfo dinmu na Nijeriya shike da daraja ta 83 a Duniya, hakanan samun bisa (watau izinin shiga kasa), shi kansa a kowane lokaci abu ne mai matukar wahala.

To sai dai, akwai kasashen da shigan su kyauta ne ba tare da wata bisa ba, ga dukkanin dan Nijeriyan da yake rike da Fasfo din Nijeriya, za ka iya shiga zuwa kowace daya daga cikin kasashen Afrika ba tare da ka wahalar da kanka da wata bisa ba. amma wasu za su bukaci ka rubuta neman bizan a lokacin da za ka shiga cikin kasar na su.

· Rwanda: ita ce kasar Afrika, mafi natsuwa, Rwanda ta kasance abar zabi ga masu zuba jari da masu zuwa yawon shakatawa. Bayan yakin kare dangi da aka yi a kasar a shekarar 1994, kasar wacce ke gabashin Afrika, a yanzun tana daukan wani sabon ado. Sannan a yanzun ta zama kasa mafi zaman lafiya a cikinta, inda take da kashi biyar kadai na masu aikata laifuka.

Ana samun biza a lokacin da za a shiga cikin kasar a kan dalar Amurka 100 guda kacal ga dukkan wani dan Nijeriya da yake dauke da Fasfo din na Nijeriya.

  · Djibouti

Kasa ce da ke gabashin Afrika, daya daga cikin waje mafi kyau domin kai ziyara daga Nijeriya ita ce Djibouti. Kila za ka bukaci biza a lokacin da za ka shiga cikin kasar, a kan farashi mai sauki, amma har yanzun kasar tana da kyawawan wurare na kai ziyara kamar tafkin Assal, wanda shi ne waje mafi zama a karkashin kasa a Afrika. A duk Duniya ma shi ne waje na uku, baya ga tafkin Galilee da mataccen tafki.

· Morocco: Al’adu, Yanayi da tsadaddun kyautuka na kasar Morokko, ne suka mayar da kasar babbar waje na masu sha’awar yawon shakatawa da kashe angunci. Akwai manyan wurare, shaguna, wuraren cin abinci da sauransu masu yawa a manyan titunan kasar Morocco,  wadanda tabbas za su ba ka sha’awa ka kai anguncinka can, wanda ba za ka taba jin takaicin hakan ba.

· Cape Berde: Wannan kasa ce da ke saman tsibiri wacce za a same ta a ammacin Afrika. Tana daya daga cikin wajen yawon shakatawa mafi ban sha’awa a nahiyar ta Afrika baki-daya, domin tana da yanayi mai kyau da kyawawan wurare wanda mutum zai yi hutunsa a cikin jin dadi.

· Kenya: Wannan kyakkyawar kasar waje ne wanda yake cike da namomin daji ababen sha’awa masu yawa, da kuma wuraren tarihi. Biranen da za a ziyarta sun hada da, Nairobi da Mombassa, inda ake samun maraba mai kyau da kuma fata tagari. Ita ma za a bukaci biza a lokacin da za shiga cikin kasar.

· Uganda: Wannan kasa da ke gabashin Afrika wacce ke da tarin tarihi da kuma tsadaddun wurare kamar su tafkin Bictoria da sauransu, ta bar ‘yan Nijeriya su iya tafiya cikinta su karbi biza a lokacin da za su shiga cikin kasar.

· Sudan: ‘Yan Nijeriya za su iya samun biza a lokacin da za su shiga kasar Sudan domin kai ziyara a cikin wannan makekiyar kasar ta Sahara mai kumshe da nau’ukan namun daji kala daban-daban masu ban sha’awa.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!