Connect with us

CIWON 'YA MACE

Kisan Gilla Ga Miji: Mata Ina Muka Dosa Ne?

Published

on

A cikin shekarun nan, kuma cikin watannin nan na kusa ana yawaitar samun matsaloli na kashe-kashe tsakanin ma’aurata wanda mafi rinjayen abin yafi ta bangaren mata ne. Shin wacce irin matsala ce da ba za a iya warware ta ba har sai an kai ga rasa rai? Shin mace da aka sani da rauni hade da tausayi, ta yaya ta samu karfin gwuiwar aikata irin wannan aika-aikar ta raba maigida da ransa don kawai wata ‘yar matsala ta faru a tsakaninsu? ‘Yar matsala za a kira dole, domin duk abin da aka kasa gyarawa ko warwarewa to rabuwa shi ya fi alheri.

Shin muna tuna irin zunuban da muke dauka kuwa ta dalilin kashe rai? Shin ba ma tunanin wannan kashe-kashe dake faruwa a tsakaninsu ma’aurata na daga cikin abin da ke kara jefa mu cikin matsin rayuwa? Tabbas wadannan fitintinu ba za ta tsaya a kan wacce ta yi kisa kawai ba, za ta zaga ta fada har kan wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Mu sa ni mace a ko ina an santa da tausayi musamman a kan abin da ta ke so, amma babu wani dalili da zai saka don yar matsala ta faru ta dauki makami da sunan daukar fansa.

Da an yi batu, wata za ta ce kishin mijin ta ke yi, ko ta ga yana ‘Chatting’ da wata, ko yana zaluntarta, da sauran abubuwa na rashin kyautatawa. ‘Yan uwa mata mu nutsu kar ya zamto a duniya mun sha wahala mu mutu mu shiga wutar jahannama ta dalilin da namiji. Ba ruwanki da wayar mijinki, haka kishi ki yi na kyautatawa, idan ya zalunce ki ki sanar da magabatanku, amma ba ki dauki makami ba. Shin mun taba zama mun yi tunanin ya rayuwar yaranmu za ta kare a shekaru goma masu zuwa kuwa? Har kullum yaranmu na koyi ne da abin da suka tashi suka tarar muna aikatawa.

Shawara…

‘Yan uwa mata ina ba mu shawara a kan zamantakewa, da ki kashe mijinki ki zama abin kwatance har jikoki gara ki nemi ya sauwake miki, ki tsira da imaninki da sauran mutuncinki a cikin al’umma. Abubuwan dake faruwa a yanzu tsakanin ma’aurata abin ya yi yawa ta yadda zai shafi rayuwar ‘ya’yammu masu tasowa nan gaba. Ki yi kokari ki zama abin koyi da kwatance wurin ‘ya’yanki dama al’umma. Kar ki sake shaidan ya zama jagora a tsakanin ragamar aurenki.

Allah ya sa mu gyara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: