Connect with us

WASANNI

Kofin Duniya Na Mata: Ba Za Mu Amsa Gayyatar Donald Trump Ba, In ji ‘Yan Wasan Amurka

Published

on

Dubban magoya bayan kungiyar kwallon kafar Amurka ta mata ne suka hallara a birnin NewYork wajen tarben ‘yan wasan bayan gaggarumar nasara da suka samu tareda lashe kofin Duniya na kwallon kafa da ta gudana a birnin Lyon dake kasar Faransa tareda doke Netherlands da ci 2 da nema.

An dai bayyana cewa ‘yan kasar na sayen rigunan ‘yan wasa dake dauke da alamomin tarmamu hudu dake da nasaba da nasarori hudu da suka samu tare da lashe kofin Duniya sau hudu da suka taba lashewa.

Wasu daga cikin ‘yan wasan yanzu haka sun bayyana cewa ba za su amsa goron gayata daga fadar Shugaban kasar Donald Trump ba saboda yadda yake sukar ‘yan kwallon kasar yayinda wasu kuma suke ganin yakamata su amsa gayyatar.

“Muna Magana akan matakin da zamu dauka akan gayyatar da muke tunanin za’ayi mana saboda kawunan ‘yan wasan ya rabu akan a amsa gayyatar ko kuma ayi fatali da abinda zaizo daga fadar shugaban kasar” in ji Rotap, kociyan tawagar kasar

Ya cigaba da “Wasu daga cikin ‘yan wasan kasar tuni suka fara jifan shugaba Trump da maganganu masara dadi yayinda shima kuma a matsayinsa na shugaban kasa yakeyin abinda baya kamata ga ‘yan wasan.

Tuni dai hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bayar da shawara ga tawagar cewa yakamata su amsa gayyatar da shugaban zaiyi musu saboda shine shugaba kuma dole sai an kai masa kofin inda kuma hukumar ta shawarci ma’aikatar wasanni ta kasar akan ta sasanta duk wani rikici tsakanin bangarorin biyu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: