Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Kori Karar Da Aka Shigar Kan Takardun Karatun Buhari

Published

on

Kotun daukaka kara dake zaune a Abuja a rfanar Juma’a ta yi watsi da karar da aka shigar kan shugaba Muhammadu Buhari inda ake kalubalantar takardun karatunsa don hanashi tsayawa takara kujeran shugaban kasa
Kwamitin alkalai uku wanda mai shari’a Tinuade Akomolafe-Wilson yake jagoranta sun tabbatar da hukucin da babbar kotun tarayya dake Abuja ta zartar na yin watsi da karar da ka shigar.
Da yake zartar da hukunci kotun daukaka karar, mai shari’a Muhammad Idris ya ce kotun tayi watsi da karar saboda an shigar da karar bayan wa’adin kwana 14 na shigar da karar ya riga ya wuce kamar yadda sashe na 285(9) na kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada.
Kalu Kalu, Labaran Ismail da Hassy Kyari el-Kuris, sun garzaya kotun daukaka kara ne bayan babban kotun tarayya tayi watsi da karar tun farko
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: