Connect with us

LABARAI

Kotu Ta Yi Watsi Da Batun Dakatar Da Nadin Alkalin Alkalai

Published

on

Wata babbar kotun Nijeriya dake zaune a birnin tarayya Abuja, a yau Juma’a ta yi watsi da karar da aka shigar gabanta ana mai kalubalantar da ta dakatar da kudurin tabbatar da nadin Alkalin Alkalai na kasa, Tanko Muhammad.

Mai shari’a Iyang Ekwo na kotun shi ne ya yi watsi da karar da ‘Omirhobo Foundation’ suka shigar da hujjar cewa ba su da hurumin ma tun farko na shigar da karar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa; shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa majalisa sunan Tanko Muhammad domin su tabbatar da shi a matsayin Alkalin Alkalai na kasa.

Sannan kuma ya bukaci majalisar da su tabbatar da nadin mashawarta mutum goma sha biyar. Shugaban majalisar, Ahmad Lawan ya karanta wasikar ta shugaban kasa a wani zama da suka yi.

An dai rantsar da Tanko Muhammad ne a matsayin Alkalin Alkalai na riko a ranar 25 ga watan Janairun shekararnan bayan dakatar da tsohon Alkalin Alkalan Walter Onnoghen da shugaban kasa Buhari ya yi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: