Connect with us

RAHOTANNI

Kungiyoyi Sun Shirya Wa Masu Magungunan Gargajiya Bita A Kano

Published

on

Cibiyar masu horar da sana’oi da kuma bunkasa ci gaba al-umma da ke karkashin Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano, YMSU tare da hadin gywiwar Kungiyar wayar da kan al’umma ta Lighthouse, karkashin Shugabancin Kwamared Iliyasu Sulaiman Dawakin Tofa, sun shirya taron bita na kwana biyu ga masu Magungunan gargajiya, wadanda suka zo daga Jihohi 19 na Arewacin wannan kasa domin wayar da kansu a kan inganta sana’ar tasu ta Magungunan na gargajiya. Musamman ta nhanyar da za a inganta su da kuma zamanantar da su, kana da yadda za a sayar da su ko tallata su a zamanance, wanda aka yi a ranar Talatar da ta gabata.

Dakta Mahabu Musa Garba, shi ne Daraktan Cibiyar ta YMSU wanda ya bayyana cewa,  babban makasudin aiwatar da wannan bita ta tsawon kwanaki biyu shi ne, yadda za a mayar da sana’ar Maganin gargajiya ya zama na zamani kamar yadda tsarin magungunan Asibiti suke a yau, ta yadda za a samu ci gaba a cikin harkar  baki daya.

A dai taron wannan bita na kwanaki biyu, YMSU ya samu halartar manyan-manyan masana da sauran masu ruwa da tsaki a wannan harka, inda kuma suka gabatar da bayanai masu zurfin ilmantarwa da ratsa jiki, domin dai amfanin mahalarta wannan bita daga wadannan Jihohi na Arewacin wannan kasa.

Dakta Nura salihu, wanda shi ne Shugaban Cibiyar Magungunan Gargajiya ta Salihunnur Traditional Medicine Center na Kasa, ya yi dogon bayani filla-filla na sassa daban-daban na gabobin dan Adam da kuma yadda suke aiki a jikinsa, inda bayanin nasa ya rika yinsa da harsuna uku day a hada da Larabci, Hausa da kuma harshe Turanci domin dai fahimtar da mahalarta taron halitun dan Adam da aikinsu da kuma yadda za a kare lafiyar kowace gaba ta hanyar Maganin Gargajiyya, yayin da wata lalura ta samu. Kazalika, Salihunnur ya kuma yi dogon bayani a kan yadda suke da ilmin ganyayyaki, tsirrai da kuma sauyoyi ta yadda suke ba da magani na cututtuka masu wuyar sha’ani cikin ikon Allah a kuma samu waraka.

Haka zalika, Injiniya Abdullahi Mai Turare daga Cibiyar kyan-kyasar Masana’antu ta Jihar Kano, shi ma ya yi nasa jawabin dangane da yadda Cibiyar ke samar da Injinan sarrafa Magunguna da sauran makamantan su a cikin sauki.

Har wa yau, Sarkin Magununa na Kano, Alhaji Rabilu Abdullahi da Hajiya Dakta Fanna kwararriya kuma masaniyar magungunan gargajiya da kuma Dakta Yakubu Mai Gida Kachako, na daga cikin wadanda suka halarci wannan taro na kara wa juna sani don inganta Magununan Gargajiya, suka kuma bayyana gamsuwarsu a kan wannan bita da aka aiwatar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: