Connect with us

LABARAI

Kwalejin Folitakanik Na Ibadan Na Shirin Kona Wayoyin Dalibai Na Miliyoyin Naira

Published

on

Hukumomin kwalejin kimiyya da fasaha ta Ibadan na shirin kona wayoyin dalibai na miliyoyin naira, wadanda aka kwace daga hannun daliban lokacin da ake gudanar da jarabawa.

Kwalejin ya dauki wannan matakin ne domin yaki da satar amsa lokacin jarabawa. Mataimakin shugaban kwalejin, Bayo Oyeleke, shi ya bayyana hakan lokacin da ya ke zanta wa da manema labarai, wannan mataki zai kara tabbatar da tsarkake harkar jarabawa a kwalejin.

“Za mu ci gaba da daukar irin wannan mataki domin mu samu damar yaye dalibai masu nagarta ga wadanda suka yi aiki tukuru.

“Muna da dokokin wadanda suka shafi jarabawa, daya daga cikin shi ne, kar wani dalibi ya shiga da wayar salula cikin wurin jarabawa, amma wasu dalibai ba sa jin magana.

“Mun kuduri cewa, duk wani dalibi da aka samu da wayar salula lokacin da ake gudanar da jarabawa, to kwalejin ta yanke hukuncin cewa, za a kona wadannan wayoyi da aka kwace,” in ji shi.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: