Connect with us

LABARAI

Kwato Dukiyar Satar Da Aka Kai Waje Na Nema Ya Gagari Kundila – Magu

Published

on

A ranar Alahamis ce, Mukaddashin shugaban Hukumar hana cin hanci da karban rashawa EFCC, Mista Ibrahim Magu, ya ce, hukumar na shi tana fafatawa ne da wata kakarfan runduna a kan yakin da take yi da cin hanci da karban rashawa.

Ya ce, hukumar na shi ta kuduri aniyar shiga yakin da cin hanci da karban rashawa har sai ta ga abin da ya turewa Buzu nadi.

Ya bayyana takaicinsa na wahalar da ke cikin maido da kudaden da aka sace aka kuma boye su a wajen kasar nan.

Magu ya yi wannan bayanin ne a wajen taro na 3 na ranar yaki da cin hanci da karban rashawa a Afrika, wanda hukumar ta EFCC ta shirya a Abuja.

Magu ya ce; “Rundunonin da muke fuskanta karfafa ne, saboda suna da kudade masu yawa da suka sata a tare da su, suna da karfin da za su iya tursasa duk wani kokarin bincike da hukunci namu, amma dai mun kuduri aniyar jagorantar yakin a kan cin hanci da rashawa.”

Magu ya ce, duk da shike dukiyoyin da aka sace daga kasar nan aka kuma boye su a wajen kasar nan, abu ne mai wuyan gaske a iya dawowa da su cikin kasar nan.

Ya ce, “Dawowa da wadannan dukiyoyin da kadarorin cikin kasar nan ya zama matsala sosai.”
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: