Connect with us

WASANNI

Lashe Kofin Afirka: Muna Bukatar Addu’a Daga ‘Yan Nijeriya – Ahmad Musa

Published

on

Dan wasan gaba na Super Eagles kuma na kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr, Ahmad Musa, ya bayyana cewa babban abinda tawagar ‘yan wasan take bukata a wanann lokaci shine addu’a domin ganin sun dawo kasa Nijeriya da kofin.

Super Eagles ta Nijeriya ta lallasa Bafana Bafana ta Africa ta kudu da kwallo 2 da 1 a wasan gab da na kusa da na karshe na cin kofin Afrika da ke ci gaba da gudana can a kasar Masar kuma yayin wasan na daren Laraba wanda ya gudana a filin wasa na birnin Cairo, Super Eagles ce ta fara zura kwallon farko a raga ta hanyar dan wasanta Samuel Chukwuze a minti na 27 da fara wasa, ba tare da Bafana Bafana ta farke ba har zuwa tafiya hutun rabin lokaci.

A minti na 71 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Bafana Bafana ta farke kwallon ta hannun dan wasanta Bongani Zungu amma dan wasan Nijeriya William Troost-Ekong ya kara kwallo ta biyu a minti na 89 gab da karkare wasa, matakin da ya bai wa Super Eagles din gagarumar nasara.

“Muna cigaba da godiya ga masoya dake Nijeriya kuma muna cigaba da samun kwarin guiwa bisa goyon bayan da muke samu daga wajen ‘yan kasa saboda haka har yanzu babu abinda muke bukata shine a cigaba da yimana addu’a” in ji Ahmad Musa, tsohon dan wasan Kano Pillars

Afrika ta kudu wadda ta fitar da mai masaukin baki Masar daga gasar, dama a tarihin kwallo tun daga 1992 sau biyu kacal ta taba yin nasara akan Nijeriya cikin haduwa 14 da suka yi a manyan wasanni.

Yayin wasan dai akalla ‘yan wasan africa ta Kudu 4 ne suka samu katin gargadi ciki har da Percy Tau, yayinda Ahmad Musa a bangaren Nijeriya shi ma ya samu nasa katin gargadin wato (Yellow Card).
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: