Connect with us

LABARAI

Mun Kammala Shiri Don Fara Horar Da Sojoji A Dajin Falgore, In Ji Ganduje

Published

on

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ahmed Iiyasu ya bayyana Gwamnan Jihar .

Dakta Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Jagoran kula da kuma samar da ingantaccen tsaro ga daukacin al’umma Jihar Kano, musamman idan aka yi la’akari da kyakkyawar aniyarsa ta ci gaba da inganta harkokin tsaro a fadin Jihar. Ko shakka babu, Gwamnatin Kano na yin duk wani abin da ya kamata don hada hannu da sauran bangarorin tsaro  a Jihar domin cimma nasarar da ake fata da kuma bukata.

Da yake jinjina wa tsare-tsaren Gwamna Ganduje, wadanda suka hada da shigo da Sarakunan Gargajiya, don tabbatar da kyakkyawan tsarin tsaro a Jihar Kano. Kazalika, Kwamishinan, ya sake tabbatar da goyon bayan Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano domin inganta harkokin tsaro da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma a kowane hali kamar yadda doka ta tanadar.

CP Ahmed, na yin wannan jawabi ne, a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a Fadar Gwamnatin Kanon tare da sauran bangarorin tsaro da suka dafa masa baya domin nuna cikakken goyon bayansu ga Gwamnan a kan harkokin tsaro.

“Mai girma Gwamna, kasancewar ka na jagoran harkokin tsaro a wannan Jiha, ko shakka babu ka dauki matakai na sauya tsohon fasalin  tsaro a Jihar Kano musamman ta fuskar samar da cikakken zaman lafiya da kuma fahimtar juna. Sannan ya kara da cewa, a shirye muke don yi aiki tare da kai domin samar da cikakken tsaro a fadin wannan Jiha baki daya, muna kuma kyautata zaton samun kyakkyawar nasara a cikin wannan aiki namu da muka sanya gaba”, in ji CP Ahmed.

Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa, tun lokacin da ya karbi aiki cikin makwanin baya da suka gabata, Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar damke mutane 660 da ake zargi da aikata laifuka iri daban-daban. Haka nan daga cikin su,  an gurfanar da 600 a gaban Kuliya.

Iliyasu, ya kuma sake jinjinawa Gwamnatin Jihar Kano, bisa kokarin da ta ke na taimaka wa Rundunar ‘Yan Sandan da abubuwa daban-daban da take bukata wanda ya shafi harkokin tsaro domin dakile aikace-aikacen batagari.

A lokacin da yake yin nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya bayyana wa sabon Kwamishinan

‘Yan Sandan cewa, zuwansa Kano ya rage yawaitar aikata miyagun laifuka a jihar, sannan ya sake jadadda cewa “babu shakka sace-sace ya ragu kwarai da gaske, barayin shanu kuma sun cika wandonsu da iska, yayin da masu fashi da makami da kuma sauran masu yin  garkuwa da mutane su ma suka yi layar zana a ciki da wajen wannan Jiha”, in ji Gwamna.

Domin kawo karshen matsalar tsaro da ke fuskantar Jihar Kano kuwa, Gwaman Ganduje cewa ya yi. “Tuni aka tsara samar da Rundunar horar da Sojoji a cikin Dajin Falgore wanda ake sa ran nan ba da jimawa ba za a ci gaba da aiwatar da wannan aikin don kuwa dukkanin wasu tsare-tsare sun kammala domin fara wannan muhimmin aiki.”

Gwamnan ya kara da cewa, yayin da masu aikata laifuka ke yin amfani da wasu Dazuka a kasar nan, ba za mu taba barin Dajin Falgore ya zama mafaka ga masu aikata irin wadannan laifuka ba. Saboda haka, wajibi ne mu sake fasalin Dajin ta hanyar mayar da shi wurin amfani a lokaci irin wannan wanda muke fatan hana masu aikata laifuka samun mafaka ko maboya, in ji shi.

Har ila yau, Gwamnan ya bayyana farin cikinsa musamman na ganin cewa, a koda yaushe akwai

kyakkyawar alaka tsakanin Jami’an tsaro da bangaren Gwamnatin wannan Jiha ta Kano. Ya ce wannan kyakkyawar halayya ce ta taimaka wa kwarai da gaske wajen inganta harkokin tsaro a Jihar Kano.

“Zan yi amfani da wannan dama in sanar da kai cewa, za mu gayyaci Shugaban ‘Yan Sanda na Kasa baki daya, ya zo nan Kano don kaddamar da aikin da muka aiwatar a Shelkwatarku ta ‘Yan Sanda da ke wannan Jiha, wanda ya kunshi ofisoshin shiyya-shiyya. Sai kuma samar da ingantaccen dakin kayan aiki irin na zamani wanda muka samar wa Shelkwatar taku”, a cewar Gwamnan, kamar yadda Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano, Abba Anwar ya Shaida wa Jaridar Leadership A Yau.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: