Connect with us

WASANNI

Mun Shirya Sayar Da Neymar, In Ji PSG

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German ta ce a shirye ta ke ta raba gari da dan wasanta Neymar matukar ta samu tayi mai kyau da zai mayar mata da kudaden da ta kashe akan dan wasan ko da kuwa daga kowacce kungiya ce.

A cewar Leonardo Araujo, manajan wasanni na PSG, kawo yanzu babu kungiyar data nuna bukatar sayen dan wasan hatta Barcelonar da ya ke fatan komawa saboda haka kofa a bude take ga duk mai son sayansa.

Neymar dan Brazil mai shekaru 27 wanda ya koma PSG daga Barcelona kan yuro miliyan 222 a shekarar 2017, har yanzu ya na da sauran wa’adin shekaru 3 kafin karewar kwantiraginsa, sai dai ya ce ya na son sauya sheka ne saboda matsalar da yake fuskanta da yanayi a Faransa.

Ko a kakar wasan da ta gabata an ga yadda Neymar ya bata kusan watanni 5 yana jinyar rauni da kuma yadda a karshen kakar wasa aka dinga dakatar dashi daga busa wasanni saboda halayen rashin tarbiyya daya dinga nunawa.

A cewar Leonardo, kungiyar PSG  bata bukatar ‘yan wasan da za su rika jin sun yiwa kungiya alfarma saboda kasancewarsu a cikinta, sai dai wadanda za su yi alfahari da kasancewar su ‘yan wasanta.

A kwanakin baya ne dai shugaban kungiyar ta PSG, Nasir Alkhilapi ya bayyana cewa kungiyarsa bazata amince da duk wani dan wasa ba wanda yake ganin yafi kungiyar kuma kowaye zasu sayar dashi domin samun kwanciyar hankali a kungiyar.
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: